An Kama Wani Mawakin Kwankwasiyya Bisa Yin Waka Mai Taken ‘A Wanki Gara’

0

An Kama Wani Mawakin Kwankwasiyya Bisa Yin Waka Mai Taken ‘A Wanki Gara’

Daga ISAH BAWA DORO

A yau Talata, 4 ga watan Fabrairu Jami’an tsaro daga jihar Kano sun kama matashin mawakin siyasar nan na jihar Katsina mai suna Muhammadu Buhari, wanda aka fi sani da “Kosan Waka”.

Kosan waka dai fitaccen mawaki ne, dan gani kashe nin Kwankwasiyya, kuma daya daga cikin mawakan Gwamnan Jihar Katsina, wanda yake wakar sa da salon Dauda Kahutu Rarara.

Ana zargin kamun da aka yi wa mawakin ba ya rasa nasaba da wata sabuwar wakar sa da ya fitar a shekaran jiya mai taken ‘A WANKI GARA’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here