INA DAN TAKARAR APC AKIDA ABUBAKAR SAMA’ILA?
Daga Taskar Labarai
Wani bincike da jaridar Yaskar Labarai ta dau tsawon wata guda tana yi shi ne gano inda dan siyasar nan na APC, da ya taba tsayawa takarar gwamna kuma yayi yunkurin sake tsayawa a 2019 yake.
Watau Alhaji Abubakar sama ila Wanda aka fi sani da Abu sama,surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma da ga hamshakin dan kasuwan nan Alhaji sama ila isa funtua
Binciken mu ya bi, mafiyawan magoya bayan shi inda aka gano wasu sun zama marayu, bayan a lokacin fadi tashin siyasar su ‘yan gata ne kullum cikin kudi da yin abin da suke so.
Taskar Labarai ta gano Abubakar ya yanke duk wata hudda da mafi yawan dakarun shi na siyasa, wasunsu har sun koma sana’o’i, wasu kuma sun koma jam’iyyar PDP.
Taskar Labarai ta gano daya daga cikin zakakuran shi a fanni yada labarai Alhaji Abdullahi Usman Tumburkai ya koma jam’iyyar PDP, rasa Tumburkai da Abu Sama yayi ba karamar asara bace da ci baya a gareshi. Don Abdullahi jan namiji ne mai kokari.
Binciken mu ya gano Abu Sama ya samu rashin lafiya kan wani hatsari da yayi wannan ya sanya ya kwanta asibiti a daya daga cikin kasashen Turai.
Ance sai da likitoci suka yi awowi akanshi har aka fara fitar da rai, Allah ya taimaka aka shawo kan lamarin. Abu Sama yana warware wa a asibiti, sai yayi zaman shi a daya daga cikin gidajen shi na kasashen waje, wanda ya dau watanni yana hutawarshi.
A lokacin ba wanda ke magana da shi sai wanda yaso ya bugo ma waya, sai wasanni motsa jiki da zuwa wajajen shakatawa da bude ido, kamar yadda wata majiya ta tabbatar mana.
Majiyarmu tace Abu Sama ya dan shigo Najeriya amma shima wata hidima ta kawo shi, yana kammalawa ya koma inda ya ke hutawa.
Wani abin da muka gano da yawa abokan siyasar shi sun fara nadamar da suka bishi an bar su kamar jemagu basu ga tsuntsu ba su ga tarko.
Su ba APC Abuja ba, ba kuma jiha kuma basa PDP. Wani daga cikin su ya fadawa jaridar nan cewa “Akan Alkawali muka bishi, cewa ko duk yadda ta kama ba zai watsar damu ba, amma kalli abin da yayi mana, Allah ya sa yace zai sake takara 2023”.
Mun memi wanda zai magana da yawun Abu Sama don fadin nashi barayin, kowa muka samu sai yace baya da wannan hurumin. Mun samu lambobin shi duk basu shiga mun aika masa sakon rubutu ta waya sakon ya isa amma babu amsa.
…………………………………………………………………………
Jaridar Taskar Labarai da ‘yar uwarta The links News jaridu ne dake bisa yanar gizo masu zaman kansu suna kuma a bisa duk kafofin sadarwa ta zamani. www.taskarlabarai.com da www.thelinksnews.com duk sako aika ga 07043777779