YAN BINDIGA SUN KONA MUTANE A KAUYEN TSAUWA SUN KAI HARI A DANKAR
Daga Taskar Labarai
Da misalin karfe 7:00pm na ranar juma’a 14/02/2020 gungun ‘Yan bindiga da suka kai a kalla su sittin dauke da miyagun makamai suka auka kauyen Tsauwa dake yankin karamar hukumar Batsari ta jahar katsina.
Inda suka dinga antaya ruwan harsasai kamar ana yakin kasa da kasa, sun harbe mutane tara (9) har lahira.
Daga bisani kuma suka bi gida-gida suna kona rumbunan hatsi, dabbobi da mutanen da suka samu a cikin gidaje, sun kona mata da yara da tsofaffi guda goma sha ukku (13) wanda ya bada jimlar mutane 23 suka kashe a kauyen.
Kafin su shiga Tsauwa sun fara shiga kauyen Dankar ne wanda yake a kan hanyar zuwa ita Tsauwa, a Dankar ne suka kashe mutane tara (9) daidai.
Sun kashe mai gadin asibiti (PHC) da marassa lafiya. Daga bisani dai shugaban riko na karamar hukumar Batsari da Sarkin Ruman Katsina hakimin Batsari tare da rakiyar Jami’an tsaro soja da ‘yan sanda sun halarci jana’izar mutanen da aka kashe a garin Tsauwa, amma su na Dankar sun taradda an tafi da gawawwakin Katsina.
Wakilan taskar labarai sun je garin sun gane ma idanunsu barnar da yan bindigar sukayi a daruruwan guda biyu..
Wakilan sun kuma ga yadda akayi wa wadansu da aka kashe a dankar wanka da Jana iza a babbar asibitin cikin garin katsina.
Binciken taskar labarai ya gano yan bindigar bangaren masu rike da makamai ne Wanda ake Kira Dangote sune ake zargin da aikata wannan ta annatin rashin imani
Binciken taskar labarai ya ji cewa yan taddar na Dangote sun samu wata matsala da mutanen garuruwan guda biyu ana cikin tattaunawa akan lamarin suka aikata wannan aika aikar ta dabbanci da rashin imani.
Ance matsalar, da ake zargin ta kawo, manya a batsari sun shiga tsakani, basu bari aka kai karshe ba suka kai wannan mummunan Harin.
…………………………………………………………………..
Taskar labarai da the links news jaridu ne masu zaman kansu dake bisa yanar gizo da sauran shafukan sada zumunta. Suna a bisa www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com lambar waya 07043777779