KARIN BAYANI KAN BELIN MUSTAPAH JARFA

0

KARIN BAYANI KAN BELIN MUSTAPAH JARFA

Eh Tabbas An Bada Belin Dan Siyasa Mustapha Jarfa Amma Ba A sake shi ba

A jiya ne dai kotun majistrate mai lamba 47 dake zaman ta a unguwar Gyadi-Gyadi ta Sanar da bada belin Dan Gwagwarmayar nan a gidajen radio wanda aka fi sani da jagoran ummati, wato Mustapha Jarfa, bayan shafe shekara guda da kusan kwanaki 49 a daure.

Kotun ta bada belin nasa ne bisa sharadin cewa sai ya kawo wani dayake da mataki na 14 a aikin gwamnati ko a karamar hukumar ko jiha ko kuma a tarayya tare da mutumin da ya biya haraji na shekara biyar, sharadi na uku shi ne ba zai yi magana a wata kafar sadarwa ba har sai an gama shari’ar.

Kotun tace Idan kuma ya tserewa kotu wadanda suka tsaya masa za su biya naira dubu dari bibiyu.

Sai dai kasancewar ba cika sharudan a lokacin ba, an sake mai da shi gidan Yari,

Karku manta dama anyi masa hukunci na shekara guda a gidan yari a kotun rijiyar zaki kuma a halin yanzu ya cika hukuncin da aka dauka masa domin ya shekara a daure sai dai munji labarin cewa belinsa aka bayar.

Daga Salisu Magaji Fandalla’fih

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here