AN BADA BELIN KOSAN WAKA

0

AN BADA BELIN KOSAN WAKA.

Daga Shafin Kannywood Exclusive

A Yau Alhamis, 27 ga watan Fabrairu 2020, aka bada belin mawakin siyasar nan na jihar Katsina mai suna Muhammadu Buhari wanda aka fi sani da “Kosan Waka”, wanda ‘yan sandan jihar Kano, suka kama a ranar Talata, 4 ga watan nan Fabrairu a Katsina suka tafi da shi Kano.

A ranar Laraba 5 ga wata, aka gurfanar da shi a kotu mai lamba 72 da ke Nomansland a Kano, inda aka tuhume shi da sakin sabuwar waƙar sa mai taken ‘A Wanki Gara’ ba tare da sahalewar Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ba.
A kotun, an zarge shi da aikata ɓatanci ga Gwamnan Kano da iyalan sa, inda har aka faɗi inda ya ambaci kalmar “Gwaggo” a waƙar, wanda laƙabi ne na matar gwamnan, Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje.
Tun a zaman farko na shari’ar lauyan da ke kare mawaƙin ya nemi a bada beli, sai mai Shari’i ya ƙi. A maimakon haka, sai ya tura mawaƙin zuwa gidan yari bayan ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Talata, 11 ga Fabrairu, 2020.

A yau ‘yan majalissun jam’iyar PDP na kananan hukumomin Kumbotso da Gezawa da ke jihar Kano suka karbi belin mawakin.

See also  ME YA HANA HADIZA BALA USMAN RIJISTA A MUSAWA?

Tun a washegarin da aka kama Mawakin ‘Kannywood Exclusive’ sun tuntubi shugaban hukumar tace Finafinai ta Jihar Kano Isma’il Na’Abba Afakallahu akan kamun da aka yi mawakin, sai dai ya ce ba zai iya magana ba, kasancewar maganar tana kotu, duk kuma abun da yake kotu, hukumar ba ta iya magana akan lamarin in ji Afakallahu.

Wannan shari’a dai ta tada muhawara musamman a Katsina inda wasu ke ganin hukumar ta wuce gona da iri, su ka ce ba ta da hurumin da za ta kama wani wanda ba ɗan Jihar Kano ba ta kai shi Kano.
Wani tsohon shugaban hukumar, wanda ya buƙaci a sakaya sunan sa kuma, ya ce: “Hukumar Tace Finafinai iya Kano ne kawai ta ke da hurumi. Idan mutum ba a Kano ya ke ba, ba ta da hurumin hukunta shi.

Amma a je Katsina a kamo shi a kai shi kotu a Kano, babu wani sashe inda aka rubuta haka a dokar hukumar.” Kosan Waka dai ya share kwanaki 24 a gidan Yari na Goron Dutse da ke Kano kafin a bada belin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here