DAKARUN DAJI SUN YI KISA A KASUWAR ILLELA.

0
339

DAKARUN DAJI SUN YI KISA A KASUWAR ILLELA.
Daga Taskar labarai
A ranar lahadi 02/03/2020 da rana tsaka ana cikin hada-hadar cin kasuwa a kauyen Illela dake cikin yankin karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, dakarun daji dauke da bindigogi kirar AK-47 suka biyo wasu ‘yan-ina-da-kmare su ukku a guje suka ratso kasuwa biye da su.

Sun kama daya suka dora shi kan babur suka tafi da shi, wasu daga cikin su kuma suka kama daya suka yi ta dukansa har ya fadi a some, sannan suka tafi suka barshi nan kwance, amma ganau ya tabbatar mana cewa, ya farfado kuma ya gudu domin ceton rayuwarsa.

Dayan kuma suka bishi har kara, wanda iske shi keda wuya sai suka sa bindiga suka bindige shi, take ya fadi ya mutu.
Wannan lamari ya tada ma ‘yan kasuwa da suka je kauyen cin kasuwa hankali, kowa ka gani neman hanyar tsira kawai yake yi.

Ammma dai har ya zuwa hada wannan rahoton bamu samu tabbacin dalilin da yasa ‘yan bindigar aikata wannan aika-aika ba.
__________________________________________________
Taskar labarai jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo www.taskarlabarai.com da kuma ta turanci www.thelinksnews.com lambar waya don Kira ko sako 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here