MA’AIKACIN NPOWER YA BAYAR DA TALLAFIN KAYA KALA 1000 GA AL’UMMAR GARIN DANKAR

0

MA’AIKACIN NPOWER YA BAYAR DA TALLAFIN KAYA KALA 1000 GA AL’UMMAR GARIN DANKAR

Daga Taskar Labari

Wani matashi mai suna Yusuf Abubakar Kofar Marusa, ya shirya gangamin tallafawa da sutura ga al’ummar garin Dankar da dakarun daji suka kai wa farmaki a kwanakin baya.

Shi dai wannan matashi ma’aikacin Npower ne wanda ya bayyana wa Taskar Labarai cewa, bayan aukuwar wanann hari da ya faru a garinsu, sai ya shoga wani hali na takaici da rashin natsuwa duba da yadda ya ga an kona muhallan mutane tare da kashe mata da kananan yara.

Wannan ne ya sa ya yi amfani da damar da ke gareshi a matsayinsa na Ma’aikacin NPower, ya tattara wadannan kayayyaki har kala dubu 1000 daga abokan aikin sa da kuma wasu bayin Allah da suka taimaka da wadannan kayyaki.

Ya bayyana cewa shugaban kungiyar “Talaka Bawan Allah” Malam Kabir Shehu Yandaki, shi ya taimaka masa da qanke wadannan kayayaki da kuma dinke wadanda suka yage tare da jigilar dauko su.

Da yake nasa jawabin a wajen kaddamar da wadannan kaya Malam Bishir Mai Daura ya bayyana cewa wannan wani abu ne da ya kamata a yabawa wannan matashi, duba da cewa shi aikin Allah, abu ne da ya kamata kowa ya sanya hannunsa a ciki, kuma irin wannan taimakon shi ya kamata gwamnati ta shigo ta rika bayar da shi kai tsaye ga wadanda abun ya shafa,ba nada wakilai ba. Ya bayyana cewa Jaridar Taskar Labarai ita ce jaridar da ke kawo sahihan labarai na wannan annoba da ke faruwa, kuma tsaye take kullum wajen kira ga matasa da su tashi tsaye su dogara da kansu da kuma samar wa kansu mafita ta yadda zasu taimaki ‘yan uwansu.

Shi ma mai garin Dankar ya bayyana matukar jin dadin sa kan wannan tallafi da dansu ya yi, ya yi kira ga sauran matasa da ke zaune a birane da su yi koyi da Yusuf Abubakar domin tallafawa yankinsu.

Da Jaridar Taskar Labari ta tambayi Yusuf kan yadda ya samar da wadanann kaya duba da cewa alawus din da ke basu matsayinsu na ma’aikatan NPower ya na daukar tsawon lokaci ma ba a biya su ba. Sai ya bayyana mana cewa, ya yi kokarin hada kayan ne ta isar da sako ga duk mai ikon basu tallafi domin taimakon wadannan ‘yan uwa namu.

Ya kuma kara da cewa wannan taimakon yanzu aka fara nemansa, kungiyar su ta Tallaka Bawan Allah na kira ga duk wani mai tsaffin kaya da zasu iya amfani ya taimaka ya basu ko ba wanki zasu gyara domin bayar da su sadaka ga tarin masu bukatar su.

Wannan gangami dai ya samu halartar mutanen yankin maza da mata da kuma ‘Yan jarida da sauran al’umma da dama. Za a iya neman Yusuf Abubakar ta wannan lambar domin bayar da tallafin kayayyaki da zasu isar ga al’ummar wadannan yankuna 07065332035.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here