YADDA BOKANYA TA HALAKA ‘YAN FASHIN DAJI DA TSAFI A JIHAR NAIJA

0

YADDA BOKANYA TA HALAKA ‘YAN FASHIN DAJI DA TSAFI A JIHAR NAIJA ~~~~Karanta kasha mamaki.

Daga Jaridar Taskar Labarai

A ‘yan kwanakin nan ‘Yan bindiga sun addabi hanyar Makwa zuwa New Bussa da ma wasu kauyukan jihar Naija.

Wannan dalilin yasa wata bokanyar Sangi ta zuciya, in da tasa aka gayyato mata maharba na yankin domin su taimaka mata wajan yakar ‘yan bindiga.

Kafin su shiga dajin, sai zanenta ya zama guguwa yayi sama, can sai ya dawo dauke da kasar inda ‘yan bindigar nan suke, sannan sai tace aka wo mata kare, da aka kawo mata sai tasa adda ta sare karen, tace da maharban kowa ya shafa ma bindigar sa jinin karen, haka kuwa aka yi.

Daga nan sai tazo da wata kwarya dauke da wani ruwan magani, tace wa maharban kowa ya sha. Da suka sha ruwan maganin nan sai ta bukaci da akawo mata yara maza guda biyu wadanda basu balaga ba domin yi mata rakiya zuwa dajin.

See also  HARIN 'YAN BINDIGA A TSAUWA, GASKIYAR ABIN DA YA FARU

Lokacin da suka shiga daji tare da maharban sai tace suyi harbi domin ‘yan bindiga su san da zuwansu, koda suka yi harbi sai ‘yan bindigan nan suka kama anta yo ruwan harsashe, amma basu ga maharban ba har harsasan su ya kare, sannan tace ma maharban su cigaba da kashe ‘yan bindiga, haka kuwa aka yi maharban nan suka shiga kasar ‘yan bindiga inda suka kashe hamsin daga cikin su, sai daya can yana ta kira kwamanda, kwamanda, wanda tasa aka kama shi da hannu aka taho dashi gari domin bincike.
Yanzu haka matar tana garin makwa ana ta zuwa kallonta. Dama hausawa na cewa tsafi gaskiyar mai shi.
Taskar labarai ta tabbatar da faruwar lamarin daga ganau, bayan ta fara samun labarin daga wani sakon da aka dauka a waya ana yawo dashi.
_____________________________________________
Taskar labarai da the links news jaridu ne dake bisa yanar gizo da sauran shafukan sada zumunta. A www.taskarlabarai.com da www.thelinksnews.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here