RIKICIN WANDA ZAI GAJI SARKIN KANO SANUSI
Daga Taskar Labarai
Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa da Jaridar Taskar labarai cewa, an samu baraka mai girma tsakanin makusantar gwamnan Kano akan wa zai gaji sarki Kano in an yi nasarar tsige shi?
Majiyarmu ta tabbatar da cewa shirin wanda aka dau lokaci ana yi wanda kuma yanzu aka tado shi baki daya. An tsara a gama da kammala shi cikin watan da ake ciki na mach.
An gabatar da koke ga majalisar dokokin Kano har guda biyu kuma majalisar an bata kwanaki bakwai ta kawo rahoton ta.
Hukumar bincike ta jihar Kano ta gayyaci sarkin, yana zuwa cikin awa ashirin da hudu zata fitar da matsayarta.
Gwamnatin Kano ta ba sarkin umurnin ya nada masu nadin sarkin da basu hakimci, wanda sune ake son ayi amfani dasu su zabi sabon sarki in an yi nasarar cire sarkin.
Duk wanna yana faruwa a kasa da mako biyu da sarkin ya yi rashin wasu makusantar sa, kuma uwaye a gare shi guda biyu, yana cikin wannan juyayi aka sake cinno masa wannan wutar.
Majiyarmu ta tabbatar mana sarki Sanusi II ya rungumi kaddarar duk abin da zai zo ya kuma mika lamarinshi ga Allah.
Wata nasara da ta fara zo masa daga Allah ita ce yadda aka samu matsala a tsakanin wadanda ake zargi da hannu ga abin dake faruwa.
Majiyarmu tace wasu na bukatar a baiwa sarkin Bichi sarautar in har anyi nasara, yayin da shugaban jam’iyyar APC ke son a ba mahaifinsa, wanda yace shi ne dai-dai sarautar ta tsaya a gidan Sanusi ke nan.
Wannan ta sanya an samu rashin hadin kai a tsakanin su, wanda har wasu na cewa da a baiwa sarkin Bichi gara a kyale Sanusi ya cigaba da sarautar.
Wata majiya ta shaida mana cewa shi kuma Ganduje an matsa masa a ciki da wajen kasar a kan ya kyale sarkin, wani tsohon gwamna ya gana da gwamnan a Abuja yayi masa maganganun da sai da suka sanya jikinshi yayi la’asar.
Wata majiya tace gwamnan ya dage akan wai sarkin yayi murabus in bai so ya tsige shi, an ce na kusa da gwamnan sun shirya koda murabus yayi zasu shigar da wasu korafi su sa a kama shi a tsare, sun ce sarkin yana waje yana watayawa ba karamin hatsari bane.
An tabbatar wa da jaridar nan cewa lamarin ya ishi kowa a manyan kasar nan, musammam yadda Ganduje baya magana daya, yana iya cewa kaza yanzu gobe ya canza.
………………………………………………………………………..,
Taskar Labarai da the Links News jaridu ne guda biyu dake bisa yana gizo ana samunsu a www.taskarlabarai.com da www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta.07043777779