An Tube Min Rawani Ba Bisa Ka’ida Ba, Amma Hakan Ba Zai Sa Na Dauki Mataki Ba, Cewar Tsohon Sarkin Kano Sunusi II

0

An Tube Min Rawani Ba Bisa Ka’ida Ba, Amma Hakan Ba Zai Sa Na Dauki Mataki Ba, Cewar Tsohon Sarkin Kano Sunusi II

Daga Comr Abba Sani Pantami

Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya ce an tube masa rawani ne ba tare da an bi ka’ida ba kuma hakan ba zai sa ya dauki mataki ba, kamar yadda PUNCH ta ruwaito.

Gwamnatin jihar Kano ta tube rawanin Sarkin Kano na 14 ne bayan majalisar zartarwar jihar ta amince.

Ya yi ikirarin cewa Antoni janar na jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da kuma Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami ne suka bada umarnin tsare sa.

Lamido Sanusi II ya ce an tube masa rawani ne ba tare da an bi ka’ida ba kuma hakan ba zai sa ya dauka mataki a kan gwamnatin jihar Kano ba, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Tsohon gwamnan bankin CBN, wanda ya samu matsala da gwamna Umar Ganduje na jihar Kano tun 2017, an kore sa daga jihar a ranar Litinin a sakamakon zarginsa da aka yi da rashin biyayya ga gwamnatin jihar.

Gwamnatin jihar Kano ta tube rawanin Sarkin Kano na 14 ne bayan majalisar zartarwar jihar ta amince.

Ta kara da cewa Sanusi baya halartar tarukan da gwamnatin ta shirya ba tare da wani dalili ba wannan ta ce wannan adawa ce.

Sanusi wanda yace an gagara bashi damar sauraro wanda hakan yasa aka tube masa rawani, ya ce umarnin kama shi, mayar da shi jihar Nasarawa daga Kano da kuma tsaresa da aka yi garin Awe na jihar Nasarawa, ya zo ne daga Abuja.

Ya yi ikirarin cewa Antoni janar na jihar Kano, Ibrahim Mukhtar da kuma Antoni janar na tarayya, Abubakar Malami ne suka ba hukumar jami’an tsaro na farin kaya da ‘yan sanda damar tsare shi. Sanusi ya ce an hantare sa tare da gaggauta fitar da shi daga fadar ba tare da ya kwashe kayan da suke mallakinsa ba.

Ya ce bayan sauke rawaninsa, wani abokinsa ya turo jirgin da zai kai shi Legas daga jihar Kano amma sai kwamishinan ‘yan sandar jihar yace a kai shi Abuja.

Sanusi ya sanar da wannan ne a karar da ya shigar a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here