YADDA SARKIN KANO SANUSI 11 YA GIRBI ALHERIN DA YA SHUKA A NASARAWA.

0

YADDA SARKIN KANO SANUSI 11 YA GIRBI ALHERIN DA YA SHUKA A NASARAWA.

Daga Taskar Labarai

A taron da majalisar zartaswar Kano tayi na yanke hukuncin tube sarki Muhammadu Sanusi II, ana zargin an kawo garin Leko a jihar Nasarawa ne, don a kai sarki in da zai cutu.

Kamar yadda aka ruwaito gari ne ba ruwa ba wuta ba hanya mai kyau, yana kusa da Kogi yana da mugun sauro da wasu kwari, wadanda in sun ciji mutum sai wajen yayi bororo
Kai sarkin Kano Sanusi II a wajen wata siffa ce ta azabtarwa babba.

Bayan an yanke shawarar tsige shi da kai shi Nasarawa, wasu ‘yan majalisar zartaswar har sun fara dariyar keta da zambo da habaici.

Taskar Labarai ta tabbatar cewa, sai gwamnan Kano ya buga wa gwamnan Nasarawa waya,ya shaida masa cewa ya tsige sarki kuma yana son a kawo shi a nan Nasarawa don zaman daurin talala. Gwamnan Nasarawa yace a kawo shi zamu karbe shi da hannu biyu.

Abin da a ba sani ba shi ne gwamnan Nasarawa aminin sarki ne, tsawon shekaru kuma sarkin ya sha taimakon shi a harkokinshi lokacin da gwamnan yana babban darakta a kamfanin Dangote, Sarki Sanusi na babban darakta a bankin first Bank suna mu’amala ta kasuwanci mai kyau, lokacin da gwamnan yana babban daraktan gudanarwa na Dangote, sarkin kuma yana gwamnan babban bankin Najeriya, suna tare Muhammadu Sanusi da ya zama sarki gwamnan yana rike da kamfanin rukunin Dangote a matsayin kololuwar darakta duk suna a tare.

Gwamnan yace a tsawon shekarunsu, basu taba ko gardama ba. Gwamnatin Kano ashe bata san cewa zata kai sarkin gidan masoyin shi kuma Aminin sa bane.

See also  ENSURING THE READINESS OF THE NIGERIAN NAVY!

A garin Awey inda aka mai do sarkin, ana kawo sarki Sanusi II yana zuwa sai yaga tun daga talakkawa har zuwa sarakunan suna bashi girma, yaga ana yi masa hidima ba tsayawa, sarki Sanusi II yana da wata dabi’a, ko kai waye in kai masa abin da yaji dadi zai ce ya gode ko kuma yace a gode maka.

Abin da sarki ya manta, shi ne shi sarkin Awey da mahaifin shi ya rasu, yana neman sarautar yayi kamun kafa da wasu makusantar sarkin Sanusi II akan a nema masa sarautar a wajen gwamnan Nasarawa. Sarki Sanusi II kuma yayi wa gwamnan Nasarawa magana wadda ta jawo aka ba shi sarkin Awey, sarautar ta garin Awey.

Sarkin na Awey ya so yayi godiya, amma in ya nemi a bashi lokaci ya zo, sai sarki Sanusi II yace “yaje ya gode ma Allah don Allah ne ya bashi tun da shi da ya yayi maganarshi ba sanin shi yayi ba.”

Allah sai ya kaddara wannan lamarin, sai gashi an kuma kawo shi, da niyyar ayi masa daurin talala garin da shi ne sanadin ba sarkin sarautar garin.

Garin Loko da Awey sun ma sarkin Kano Sanusi II karamci sun kuma nuna masa kauna, kuma tabbas zasu girbi Alherin da suka aikata kamar yadda makusanta sarkin Kano Sanusi II ke fada.
……………………………………………………………………..
Jaridar taskar labarai da The links news jaridu ne, masu zaman kansu dake bisa yanar gizo da sauran shafukan sada zumunta na Facebook, inganta da sauran su.07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here