SHEKARA 30: ALMIZAN CE JARIDA MAFI DOGON TARIHI A TSARARRAKI

0

SHEKARA 30: ALMIZAN CE JARIDA MAFI DOGON TARIHI A TSARARRAKI

Kamar jiya ne muke kwanan aiki a ranakun Laraba (production day) a wani ofishi da ke kan titin Jama’a cikin Doka (garin Kaduna). Babban Edita Malam Ibrahim Musa zai tanadar mana kayan shayi, mu yi ta sha a yayin da nake sub-editing (gyaran farko) shi kuma yana editing (gyaran qarshe na rubuce-rubucen jaridar). Da yake a lokacin ban saba ba, sau tari barci yakan yi awon gaba da ni. Shi kuwa zaqaqurin dan jarida ne mai juriya, don haka sai ya hada da nawa da ban yi ba, da nasa, duk ya gyaggyara su ba tare da ya nuna bacin rai a fuska ba bare ya yi qorafi.

Wajejen 2001 na yi aikin na sub-editor (muqaddashin edita) a jaridar ta ALMIZAN, shekaru 19 ke nan baya. Na yi aikin ne ba a matsayin dan buraza (almajirin Malam Zakzaky) ba, kamar yadda sauran ma’aikatan suke, sai a matsayin dan jaridan da ya zo daga wani gidan. Na kuma qaru matuqa da aiki da Malam Ibrahim Musa. Domin ya san aikinsa, yana da basira, yana da juriya, yana kuma da haqurin zama da jama’a.

Wadannan halaye na Malam Ibrahim Musa sun kyautata alaqata da jaridar, musamman wurin rabuwa ba mu yi uwar watsi ba. Saboda ni wani samfurin mahaukaci ne na daban in ba yanzu da nake qoqarin gyarawa ba. In na ga wani babba ya yi abu mara kyau, sai na ce wai sai na gyara masa don hauka irin tawa. A wancan lokacin mun yi ta gardaddami da sukar ra’ayin juna a zaman nazarin jaridar bayan wallafata (editorial meeting) ni da marigayi Alhaji Danlami, mutumin da shi ne ya riqa daukar nauyin wallafa jaridar a lokacin. Amma albarkacin dattakon Malam Ibrahim Musa, da rabuwa ta zo, cikin raha da barkwanci aka qare. Ya yarda ya bi da ni a yadda nake na wanda ba buraza ba bare ya san ladubban bin umurnin Malam ko gujewa abin da zai saba manufar Harka duk kuwa da aqidata ta son wai a yi jaridar a jaridance sabanin mai manufar da take son isarwa. Ban qara gane girma da dattakon Malam Ibrahim Musa ba sai da na zama editan ALMAUZUUN da AHLULBAITI. Allah Sarki! Allah ya jiqansa ba don ya mutu ba. Samun mutum mai iya zama da mutane irinsa wallahi sai an tona, tonawar ma, ba sama-sama ba, can ciki.

See also  YA KASHE SAMA DA NAIRA MILLOYAN 43 A TALLAFIN AZUMI A JIHAR KATSINA

Kada a ji ina ta ambaton Malam Ibrahim Musa alhali jigon rubutun a kan ALMIZAN ne, abin da mutane ba su sani ba shi ne, ALMIZAN ita ce Malam Ibrahim Musa, Malam Ibrahim Musa shi ne ALMIZAN. Shi ne jaridar a jaridance, domin iliminsa da fikirarsa ce suka samar da ita. Kazalika shi ne jaridar a dabi’ance, domin juriyarsa da haqurinsa ne suka wanzar da ita.

ALMIZAN ta ga fitintinu iri-iri tun daga na cikin gida, har zuwa na gwamnati. A zamanin Abacha, jaridar ba ta da ofishi guda da ake yinta saboda tsabar zille wa jami’an tsaro. Sau tari babu kudin cin abincin yin aikinta sai dai na wallafarta kawai, a haka kuma za a haqura da abincin a wallafa ta don imani da aqida.

Wannan ya sa jaridu irin su HOTLINE, RANA, FITILLA, REPORTER, SENTINEL, CITIZEN, JUST da wasunsu da dama a nan Arewa suka mace suka bar ALMIZAN har yanzu. Wasu ta taradda su amma suka mace daga baya, wasu kuma ita ce suka tarar amma suka mace suka barta. Imani da aikin irin na ma’aikatanta, Malam Danjuma Katsina, Malam Umar Samaru, Malam Musa C.A., Marigayi Malam Abubakar Almizan, Malam Aliyu Saleh, Malam Ali Kakaki, Malam Hassan Muhammad, Malam Zubairu Lawal, Marigayi Malam Tahir Isma’il Gwantu da wasunsu da ban samu ambatowa ba, imanin wadannan bayin Allah ya taimaka wa dattakon Malam Ibrahim Musa har jaridar ta kafa wannan tarihi mai ban mamaki ga wanda ya san wahalar da ake sha a kan samar da gidan jarida.

A yanzu haka dai ALMIZAN ce jaridar da ta fi kowace jaridar da ba ta gwamnati ba dadewa a Arewa. Ta gwamnatin ma TRIUMPH ce kawai ke gabanta, domin su NEW NIGERIAN DA GASKIYA TA FI KWABO sun kwanta dama.

Bisa ga wannan qwazo da juriya, a kuma daidai lokacin da jaridar ta yi bikin cika shekara 30 da kafuwa, nake sara wa jaridar, da Malam Ibrahim Musa, da kuma wadancan ma’aikata da na ambata a baya. Lallai akwai abin koyi daga rayuwarsu mai albarka ga mutumin zamanin nan mai gaggawar isa ga nasara.

Muhammad Bin Ibrahim
16/03/2020

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here