KASAR IRAN TANA CIKIN LOKACI MAFI WAHALA A TARIHI
Daga Mujtaba Abubakar
Suna cikin tsananin bukatar Addu’ar Muminai, kasantuwar an maida su saniyar ware a Duniya duba da yanayin duniyar yau b ubu wata kasa da zata rayu da Independently ba tare da International trade ba ko America ko China Basu Isa ba.
Amurka ta maida Iran saniyar ware a duniya saboda kin yarda su mikawa kafirci wuya, abun yayi tasiri a tattalin arzikin kasar.
Ana tsaka da wannan yanayi Annobar Corona ta bulla a duniya bayan China sai Iran wannan babbar masifa ce wacce daya daga cikin kasashen Turai ne haka ta faru za su tsayar da komai a kafafen yada labaran su Dole ka karanta ko ka saurara ko ka kalli abinda suke so.
Iran tana cikin Halin Lahaula, domin takunkumi ya hana hatta magunguna shiga kasar ga shi suna cikin yanayin bukata, haka har tasa su ka yi wa duniya hannunka mai sanda cewa “Ofar temako bisa yadda ajalisar dinkin duniya ta tsara yayin da Bala’i ya aukawa wata kasa na Iran a bude yake” suna bukata banda na Amurka da Israel,
Ministan harkokin waje Zarif yayi kira da kasashen Turai su sa kafa su yi fatali da takunkumin Amurka a lokacin tsanani
Karshe kasashen tTurai sun yi kunnen uwar shegu da su, wanda haka yasa Zarif ya kara cewa, Iran ba zata taba zurawa kasashen Turai Ido ba a lokacin tsanani duk da nuna musu kiyayya da su ke yi.
Zuwa yanzu a kalla mutum 17000 ne suka kamu 1100 sun yi shahada 5460 sun warke.
Masana a ciki da wajen Iran na hasashen miliyoyin Iraniyawa na fuskantar barazanar kamuwa da wannan cutar idan duniya ba ta yi wani abu akai ba.
Ubangiji Allah ka kawo musu dauki albarkacin wilayarsu ga Ahlilbait (as)