KOTUN KOLI TA FITAR DA RANAR YANKE HUKUNCIN SHARA AR KATSINA
Daga Jaridar Taskar Labarai
Taskar labarai ta samu tabbacin cewa a ranar 21 ga watan afrilu na 2020 kotun koli wadda daga ita sai Allah ya isah zata yanke hukuncin shara ar dake gabanta na kananan hukumomin katsina da jam iyyar PDP suka kai cewa an rushe su ba bisa kaida ba.
Shara ar da ake ta tafkawa tun a shekarar 2015 shugabannin kananan hukumomin katsina, zababbu karkashin jam iyyar PDP suka kai gwamnatin katsina ta APC kara cewa an rushe su ba bisa kaida ba.
Shara ar an fara ta tun daga babbar kotun tarayya ta jaha,ta kai har zuwa kotun daukaka kara, duk kotunan suna korar karar.abin har ga kotun koli da ta Sanya 21 ga watan afrilu Zata yanke hukuncin ta.
Wannan shara a itace ta kawo kiki kaka na kasa yin zabe a katsina, gwamnati na jin tsoro taka dokar kotu in tayi zaben
Taskar labarai ta gano kotun ta koli ta sanarwa duk bangarorin a rubuce,ta shirya yanke hukuncin a ranar 21 ga watan afrilu
Kowane bangare, yana addu ar Nasara a tare dashi gwamnati na da hujjojin da suka dogara dashi.jam iyyar PDP na da nat hujjojin wasu Shari un da kotun kolin ta yanke kwanan nan akan kananan hukumomin.
Taskar labarai ta gano da yawa kansiloli da ciyamomin PDP da ake ma wannan shara ar sun koma APC . A wani tsari da zama da akayi tayi dasu a baya.
Har wadansu suka ayyana nisanta kansu da shara ar.ko in nasara ta zo bangarensu ya za a kare ? Idan nasara kuma ta kaya a barayin gwamnati ko cikin wata nawa zata yi zabe? Koma akwai kudin zaben?
Shara ar nan taci kudi ba kanana ba, ga lauyoyin da daukar nauyin tafiyar da ita.zuwan ta karshe sauki ne ga jahar baki daya.
…………………………………………………………………………
Taskar labarai da the links news jaridu ne masu zaman kansu dake bisa yanar gizo suna akan shafukan www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com 07043777779