Kawo Sabon Tsarin Sarrafa Kudi:

0

Kawo Sabon Tsarin Sarrafa Kudi:

Jajircewar Akanta-Janar na Katsina, Alhaji Malik Anas

Sharhin jaridar The Links News

Bayan sake zabar Gwamnan Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari a shekarar 2019, ya zo daidai da karewar wa’adin kujerar babban Akanta-Janar na Jihar, gwamnatin na da bukatar samo wani masanin aikin da kuma yadda aikin ke tafiya daidai da zamani, wanda zai iya kawo canji a aikin Jihar, ta kara ririta dan abin da take da shi, kuma ta kara samun wasu na shigowa.

An dau watanni ana lale da lalewa. Daga karshe Gwamnan ya ba da sanarwar ya amince da bai wa Alhaji Malik Anas wannan kujera ta Akanta-Janar.

Malik ya fada a bigire daban-daban na wannan matsayin da ya samu. Na farko matashi ne, shi ne Akanta-Janar mai karancin shekaru irin nasa da ya taba rike wannan mukamin a Jihar, kuma yana cikin masu karancin shekaru masu rike da mukamin a kasar nan. Na biyu duk rayuwarsa ta aiki a Ma’aikatar Kudi ya yi ta. Ya san ta, ya kuma san sirrin, ya san mutanen kamar bayan hannunsa. Ba wata wala-wala da za a yi masa a aikin ko gidan da yake aikin. Na uku ya san aikin, kwakwalwarsa na ja. Ko makiyinsa ya san Malik ya san aikin. Na hudu kullum yana kara wa kansa ilmin sanin aikin a kan yadda yake tafiya da zamani. Na biyar mutum ne mai kishin Jiharsa, wanda duk rayuwarsa tana cikin Jihar ba ya je ka ka dawo, a’a sai dai in an je aiki a dawo gida, kuma ya saba kawo wa Jihar wasu abubuwan ci gaba. Wani ma abin da ya kawo duk arewacin kasar nan babu kamar sa.

Wadannan dalilai ya sanya zaben da Gwamnan Katsina ya yi wa Malik matsayin Akanta-Janar na Jiha ya zo da murna da farin ciki ga mafi yawa, amma kuma cikin wasu ya duri ruwa.

Tsarin farko da Malik ya yi kokarin kawowa a Jihar shi ne shigar da Jihar sabon tsarin kudi na zamani, wanda yin haka zai samar wa Jihar wasu kudi kyauta har Dala milyan biyu in har ta shiga cikin duk tsarin da kuma ka’idar. Zai kuma samar mata da wasu damarmakin na samun wasu damar tsari ne, kamar canza layin tafiyar da al’amari daga ‘Analogue’ zuwa ‘Digital.’

Kowa ya san yadda duniya ke canzawa da gudun tsiya yanzu, hatta amsar kudi ana son komai ya koma a kan kati ne da kuma turawa.

Lokacin da Malik Anas ya karbi mukamin Akanta-Janar ya iske Jihar ba a fara komai ba a kan wannan tsarin. Ya gamsar da Gwamnan Katsina da sauran hukumomi amfanin shigar Jihar wannan tsarin. Ya kuma fara aiwatar da shi. Wannan ce matsalar farko da Malik ya fara samu a aikinsa, domin tsarin zai toshe duk wata kafa ta zurarewar kudi ta barauniyar hanya. Duk wani Kwabo sai an san ina ya tafi, wa ya yi amfani da shi. Tsari ne na dakile cin kudin al’umma a bagas, aikin zai kai Jihar Katsina tsarin kudi da duniya ta yarda da shi, kuma zai bude kafa masu tallafin kasa da kasa su dauki Jihar a matsayin mai bin ka’idar kashe kudi na duniya, kuma su shigo a yi aiki da su.

Kokarin Malik na aiwatar da wannan tsarin ya sa tsoro da girgiza ga ’yan ci-ma-zaune na Jihar da ’yan dibar ganimar haram suka fara tunanin ya za su yi wa shirin na Akanta-Janar kafar ungulu.

Matsala ta biyu da Malik ya tarar ita ce, kungiyar wasu gungun ’yan ci-da-karin albashi da aringizo da kuma saka albashin da babu. Wasu mutane ne wadanda sun raba kansu a wurare daban-daban, suna kuma aiki tare, a tsanake, kuma a cikin dibara, sun san yadda suke karawa wasu kudi, su kuma bi su amsa bayan an kammala albashi. Ko su hau sunan wani da ya yi ritaya, ko ya mutu, ko ya canza wurin aiki su rika amsar albashinsa.

Tsari ne na cuta da cin kudin Katsina da ake yi a ilmance, kuma a tsanake ta amfani da bayanan da ake da su na ma’aikatan da ke cikin rumbun ajiye bayanai na ma’aikatan Jihar Katsina.

Jaridar THE LINKS NEWS a bincikenta na rubuta wannan sharhin ta ga wadanda aka kara wa kudi, ta ga wadanda aka kara wa albashi, ta ga wadanda sun ce sun tuba, amma an taba hada kai da su a wannan mummunan aikin.

Malik Anas na zuwa ya fito da tsarin da sai an kakkabe wannan mummunan aikin, ko a rage shi ko aka dakatar da shi zuwa wani lokaci, kafin masu yi su canza salo.

Binciken THE LINKS NEWS ya gano yadda aka samu rarar kudi masu yawa daga fara wannan tsarin, wanda za a iya yi wa al’umma aiki da abin da suka ragu, amma fa ya jawo masa karin bakin jini da batanci daga wadancan ’yan kadan din, wadanda da sun samu kudin ba aikin Allah ko na Annabi suke yi ba, sai dai su hole da jin dadi da watayawa. Wasu ma ko iyalinsu ba sa amfana da haramiyar.

Wani tsari da Malik ya kafe a kan yin sa shi ne, kowane kudin aikin da Jihar ta bayar ga kowa ba a biya hannu da hannu, a’a sai dai a biya cikin asusun kamfanin kamar yadda dokar tattalin arziki ta tsara, kuma sai an cire wa gwamnatin Jiha Katsina cikakken hakkinta na doka, wato haraji da sauransu.

Wannan ya fusata ’yan kashe-mu-raba na cikin gwamnatin, kuma ya samarwa da gwamnatin kudin shiga, ya kuma sanya duk kudin Jihar an san inda suke tafiya a tsanake duk wata.

Masu kamfanonin bogi da ’yan aringizo da kashe-mu-raba sun yi Allah wadai da wannan tsarin, suna kuma guna-guni da kamfen na bata suna.

A sabon tsarin tafiyar da tattalin arziki na Katsina, Jihar ta shiga sabon tsarin duniya na kuma kasa da kasa da babu wannan da kudin Katsina suna iya kasa da abin da take samu a kason gwamnatin Tarayya, amma da wannan kokarin na Malik da jajircewa tasa za ta tsaya matsayin ta har ta kusa tarar da sa’o’inta na abin da ake ba ta dauni daga asusun kasa, wanda ake raba wa Jihohi duk wata, wanda da shi suka dogara wajen albashi da gudanarwa.

Harkar tafiyar da kudi sirri ce, kuma in aka matsa a magana kanta ana iya tono kashi mai doyi, amma wannan kadan ke nan daga nasarar da gwamnatin Katsina ta samu wajen kawo canji a Ma’aikatar Kudi ta Jihar Katsina

An fassaro daga jaridar THE LINKS NEWS wadda yar uwace ga jaridar taskar labarai da ke kan sakar sama (Intanet) a www.thelinksnews.com da kuma www.taskarlabarai.com. da sauran shafukan sada zumunta. 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here