HAKA GANDUJE KE MULKIN KANO?

0
359

HAKA GANDUJE KE MULKIN KANO?

Daga Danjuma Katsina

Wani hoton bidiyo da ke yawo a yanar gizo wanda kuma wasu manyan jaridu suka wallafa hoton na bada labarin da tambayar ko haka gwamnan Kano Alhaji Dakta Umar Ganduje ke tafiyar da mulkin Kano?

Bidiyon wasu matasa ne, dake aikin neman abinci a garin madalla ta birnin Abuja, jin cewa shugaban kasa ya bada shelar rufe Abuja na tsawon sati biyu, ba shiga ba fita, kar yunwa ta karsu suka sami wani direban babbar kanta ya dauko su zuwa Kano gida.

Sun ratso duk hanyoyin ba tare da wata matsala ba, har da Kaduna in da ake da kublen ba shiga ba fita, wata kila kowane shingen jami’an tsaro suka zo in suka fahimci halin da suke ciki sai tausaya masu su kyale su su wuce.

Cikin taimakon Allah sun iso har cikin Kano, sai ga tawagar gwamnan Kano suka tare su, matasan na ganin gwamnan sai suka fara yi masa kirari sai baba suna jin dadin sun ga mai ceton su daga halin da suka baro da wanda zasu shiga.

In da aka fara abin kamar wasan kwaikwayo sai mai girma gwamnan yace, “duk ku sabko.. ” sai wani cikin tawagar ta gwamna yace, “a’a direban kawai zai sabko” sai gwamnan yace, “haka direban ya sabko”.

Da Direban ya sabko sai yayi bayanin daga inda ya dauko su, da dalilin hakan, sai gwamnan yace, “a kai su ofishin yan sanda” ( Wanda shi ne mataki mafi kyau) sai wani da rigar karota ya tari gaban gwamnan yace, “a’a a maida su inda suka fito” sai gwamnan yace, “a mai da su inda suka fito”.

Nan ne bidiyon da ke yawo ya kare. Amma labarin dake yawo shi ne jami’an karota sun raka su don fitar da su daga Kano.
Shin wanna shi ne matsayar da ta dace?

Shin haka ake tafiyar da Kano wasu ke cema gwamnan da aka zaba mai cikakken iko ga abin da zai yi?

Su waye ke kusa da gwamnan nan suna masa shifta kamar yadda hoton bidiyon nan ya nuna?

Wannan tambaya ita ke yawo a kwalwata har ta sanya nayi wannan rubutun.

Danjuma Katsina shi ne mawallafin wasu jaridu guda biyu dake bisa yanar gizo jaridar Taskar Labarai da kuma The Links News dake a www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com. ana samun shi a 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here