SUN KAI FARMAKI HAR SUNYI KISA.
Daga Taskar Labarai
A ranar lahadi 29/03/2020 da dare wasu da ake zaton ‘yan bindiga ne suka kai hari wani kauye da ake kira Akata dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Harin yayi sanadiyyar rasa rayuwar wani bawan Allah mai suna Mallam Bawa, sanan su ka yi awon gaba da garken tumakin sa.
Mazauna kauyen sun tabbatar mana cewa lokacin da suka shigo garin basu zarce ko ina ba sai gidan Malamin wanda suka harba ga cinya, amma bai mutu ba sai bayan kwana daya da faruwar lamarin.
A wani labarin kuma ‘yan bindiga sun yi gaba da shanun (ga’i) wani mutum mai suna Mallam Haro dake zaune a Tudun wada, wani kauye da baifi nisan kilomita biyu ba daga garin Batsari. Lamarin ya faru ne ranar litanin 30/03/2020 da misalin 10:00pm na dare.
Mazauna Batsari sun ji karar harbe-harben su lokaci da suka kai harin amma ba wanda ya zaci mahara ne ganin yadda kauyen ke gab da mazaunin sojoji dake samar da tsaro a yankin Batsari da kewaye, dalilin da yasa kowa ke tsammani ko sojojin ne ke wani atisaye.