YAN BINDIGA SUNKAI HARE-HARE A WASU KAUYUKAN BATSARI.

0

‘YAN BINDIGA SUNKAI HARE-HARE A WASU KAUYUKAN BATSARI.

Daga Taskar Labarai

Da misalin 12:00am na daren ranar lahadi 05/04/020 yan bindiga masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da satar dabbobi suka kai hari a kauyen ‘Yan Dakarun, dake yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Inda su kai ta yin luguden wuta, sannan suka sace wayoyi a wani shagon caji, tare da shiga gidajen mutane suna yi masu sata.

Daga karshe kuma suka yi garkuwa da mutane biyu watau Salele Dan Maliki, bayan sun yi ma iyalinsa dukan kawo wuka, sai wata yarinya ‘yar kimanin shekara goma ita ma sun yi garkuwa da ita.

Haka kuma, daidai wannan lokacin da suke aiwatar da sana’ar tasu a ‘Yandaka, wasu kuma suna wani kauye mai suna Tudun Raha dake kudancin kauyen ‘Yan Daka can ma suna ta ruwa harsashe, sannan suka yi awon gaba da shanu da tumakin kauyen, sannan sun harbi mutum biyu; daya a Tudun raha daya kuma a wajen garin ‘Yandaka, dukkan su suna babbar asibiti ta Batsari suna jinya.

See also  CIN AMANAR KASA: SOJAN DA AKE ZARGI DA HANNU CIKIN HARIN NDA YA ZO HANNU

A wani labarin kuma, duk a cikin daren sun kai hari wani kauye mai suna Tudun Modi dake kudancin Batsari, inda nan ma suka yi ‘yan harbe-harben su na al’ada sannan suka yi kokarin satar wasu dabbobi amma mutanen kauyen sun kore su ta hanyar yekuwa da neman agaji daga nesa, su kuma suna harba bindiga har dai suka tsorata suka gudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here