HARE-HAREN ‘YAN BINDIGA NA KARA TA’AZZARA A YANKIN BATSARI.
Daga taskar labarai
A daren ranar litanin 06/04/2020, da misalin 10:00pm barayin shanu suka mamaye kauyen Dan Alhaji dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina. Da yake mutane sun samu labarin cewa za’a kawo harin, sai suka yi kokari suka kauda dabbobin su zuwa wasu kauyuka dake makwabtaka da su, sannan duk suka fice suka bar garin.
Lokacin da barayin suka shigo garin, sai suka fahimci ba kowa a garin, daga nan sai suka bi kauyukan garin suka tattaro shanun da aka kai masu ajiya suka kora zuwa daji. Mazauna garin sun tabbatar mana cewa an samu shanu biyu sun kubuto daga hannun barayin sauran kuma sai a lahira.
Haka kuma ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Watangadiya dake yammacin Batsari duk a ranar ta litanin da misalin 01:30am, inda suka fara shiga gidan wani bawan Allah mai suna Murtala Bagobiri, da shiga gidan sai suka fara yanke igiyar dabbobi shanu da tumaki.
Ganin haka mai gidan yayi kuwwa domin neman agaji, sai daya daga cikin barayin yayi harbi sama kwa-kwa…. Sai kuwa al’ummar gari suka yo waje suna kuwwa. Da barayin nan suka fahimci dai rana ta baci, sai suka yi yamma a guje suna harbo harsashe jama’ar garin kuma suna maida gami da yan bindigogin su na toka.
…………………………………………………………………………
Jaridar taskar labarai, jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da kuma yar uwarta ta turanci The links news dake a www.thelinksnews.com don labari gaggawa Kira ko tura sako a 07043777779