KOTU TA DAKATAR DA JAM’IYYAR PDP TA JIHAR KATSINA DAGA YIN ZABEN SHUGABANNIN JIHA

0

KOTU TA DAKATAR DA JAM’IYYAR PDP TA JIHAR KATSINA DAGA YIN ZABEN SHUGABANNIN JIHA

Daga Taskar Labarai

Wasu ‘yan jam’iyyar PDP a jihar Katsina karkashin jagorancin Alhaji Dauda Kurfi sun kai jam’iyyar PDP kara a kan kotu ta hana ta gudanar da zaben shugabannin ta na jiha har sai an gama jin koken su da karar da suka shigar.

Su Dauda Kurfi sun yi korafin cewa sun sayi fom daga ofishin uwar jam’iyyar amma, ofishin jam’iyya na jiha ba zai masu adalci ba, da wasu korafe-korafen.

Akan haka suna rokon kotu ta dakatar da duk wani yunkurin yin zaben shugabannin na jiha.

Kotu ta saurare su, kuma ta amince ma bukatar su in da ta bada wannan umurni ga jam’iyyar da kar ta kuskura tayi wani zaben shugabannin jiha har sai ta gama sauraren karar dake gaban ta.

Taskar Labarai taga takardar karar da kuma ta umurnin kotun. A baya ma akwai wata karar da wani dan takarar mai suna Bashir Gafiya ya shigar wanda har kotu ta bada wani umurnin.

Sannan wani bangaren PDP sun shigar da korafe-korafe ga kwamitin bin kadin zabubbukan da aka yi na shugabannin jam’iyyar na unguwanni da kananan hukumomi.

Bangaren PDP dake ja da shugabannin masu ci, fatan su kar ayi zabe har zangon mulkin na shugabannin masu ci ya kare, wanda in ya karkare dole a koma tsarin mulki a yi ma jam’iyyar shugabannin riko. Wadanda zasu sake lalen jam’iyyar.

Duk wannan hayaniya ana yin ta ne, don zaben 2023, wanda ake zargin Yakubu Lado yana son sake neman kujerar gwamna a PDP kuma har yana ta ganin ya zai rike jam’iyyar a hannunshi.

Wadanda basa goyon hakan, suke ganin tun kafin ayi nisa gara a taka ma kudurin nasa burki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here