RARARA YA BA MAI ASHARALLE KYAUTAR MOTA.

0

RARARA YA BA MAI ASHARALLE KYAUTAR MOTA.

A jiya Talata ne Fitaccen Mawakin Siyasar kasar Afrika Dauda Kahutu Rarara ya ba Gambon Surajo Mai Asharalle kyautar Mota a garin Katsina.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da mawakin ya fara yi wa ‘yan uwansa mawaka kyautar abun hawa ba.

In dai ba a manta ba, a cikin watan da ya gabata ne Rarara ya saka gasa inda zai raba kujerun Makka da Umara da motoci, da kudade kyauta ga mawaka

Rarara ya saka gasar ne don nuna farin ciki game da nada Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano da gwamnatin jihar ta yi.

Ya ce a ka’idojin shiga gasar ana so duk wani mawakin Hausa da ya ke Nijeriya ko wajen ta da ya yi sabuwar waƙa ga sababbin sarakunan Kano guda biyar, wato na Kano da na Bichi da na Karaye da na Sarkin Gaya da na Rano.

A ka’idojin, ana so kada wakar ta wuce minti biyar, sannan ya kasance a cikin minti biyar din nan mawaki zai yi wa kowane sarki wakar sa, cikin salo da zai burge kowace fada, da kuma su kan su sarakunan.

Wata ka’idar ita ce tilas ne duk mawakin da zai shiga gasar ya kasance ya na da rajista da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.

Bugu da kari, mutum 50 kacal za a zaba a matsayin zakarun gasar.

A cewar sa, a ranar da za a fidda zakarun kowane mawaki zai zo da wakar sa a rubuce kuma ya rera ta a gaban manyan baƙin da za su halarci taron, cikin su har da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Rarara ya bayyana cewa ya tanadi farfesoshin nazarin harshen Hausa da za su zama alkalan gasar.

Ga jerin sunayen kyaututtukan da zai ba Mawakan su ka yi nasara:

Na 1: Mota
Na 2: Mota
Na 3: Kujerar Makka
Na 4: Kujerar Makka
Na 5: Kujerar Umara
Na 6: Kujerar Umara
Na 7: Keke Napep
Na 8: Keke Napep
Na 9: Babur
Na 10: Babur.

Sauran mawakan 40 kuma kowannen su za a ba shi kyautar N100,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here