ZUWA GA ‘YAR MU

0

ZUWA GA ‘YAR MU

Daga Taskar Labarai

Sanarwa

Duk litinin Taskar labarai zata rika kawo maku labarai masu darasi da ratsa zuciya, da fatan za a amfana da hikimar dake cikin hikayoyin da za a rika bada wa.

A yau zamu fara da wani labari da Danjuma Katsina ya nakalto da fassaro shi daga asalin sa na Turanci zuwa Hausa, don amfanin masu bin jaridar nan mun sanya wa labarin suna “zuwa ga ‘yar mu”. Asha karatu lafiya da fatan za a tattauna ilmin dake ciki.

ZUWA GA ‘YAR MU.

A kasar Holland wani mutum da matarsa suka shirya zuwa hutu na wata guda a cikin irin jirgin ruwan nan na shakatawa, sun yi auren soyayya, kuma suna rayuwa cikin farin ciki har sun samu diya mace mai shekaru hudu a lokacin.

Da zasu tafi suka bar ‘yar tasu a wajen danginsu kafin su dawo. Don lokacin yarinyar na makaranta ba abada hutun karatu ba.

Suna a cikin jirgin sai matsala ta samu jirgin ya tsage yana shirin fashewa, kaftin din jirgin yayi duk dubarar da zai yi ya kasa sai ya shelanta cewa jirgin zai nutse nan da mintuna arba’in da biyar. Ma’aikatan jirgin suka shelanta cewa rigunan hana nutse wa ruwa da suke dasu basa isa don haka, duk mutum biyu daya za a basu, cikinsu suyi shawarar wa zai sanya wa za ya hakura?

Duk mata da miji da aka ba, sai mazan su ba matan amma, shi sai matar da kanta ta sanya wa mijin tana kuka yana kuka, suna rike da junansu har jirgin ya fashe suna rike da juna matar na bashi sakon ni, da nasiha, har karfin ruwa ya rika jan ta, tana nutsewa a hankali shi kuma yana lilo akan ruwa a hankali hannun ta ya sullube tayi kasan ruwa ta mutu shi kuma mijin yayi ta lilo har aka zo aka kawo masu dauki aka tseratar dasu.

Bayan ya dawo gida sai aka yi ta yada cewa, ya bar matarsa ta mutu don shi ya rayu, yayi gum bai fada wa kowa ya aka yi ba, ya nemi aure aka hana shi.

Ya ba ‘yar sa ilmi da kulawa da ta fara girma sai ta rika jin wadancan labaran sai taji ta tsani mahaifin nata. Ta tambaye shi ya kasa bata wata amsa, sai taji bata kaunarsa, ta rika yi masa rashin kunya shi kuma ya yi ta hakuri da ita, har ta gama jami’a ta samu aiki ba ruwan ta da shi, saboda tana jin shi ya kashe mata mahaifiya don ya rayu.

Ranar nan ya kwanta rashin lafiya, aka fada mata tace a kai shi asibitin marasa galihu,y a mutu aka fada mata tace Allah raka taki gona. Aminai kawai suka halarci binne shi.

Sai aka sheda ma diyarsa cewa gidan shi gwamnati zata amsa ta ba wani don haka tazo in akwai abin da take bukata cikin kayan shi, ta dauka, sauran kuma a kona. Tace bari tazo kila cikin kayan mahaifiyar ta taga abin tarihi da zata ajiye tana kallo.

Da tazo gidan cikin kayan mahaifiyar sai taga wani akwati karami an rubuta ga ‘yar mu daga mahaifiyarki Jessica tana buda akwatin taga wata wasika wadda mahaifiyarta ta rubuta, sai ta fara karantawa.

“Zuwa ga ‘yar mu.
Na san lokacin da wasikar nan zata same ki, bani duniya na mutu, likitoci sun same ni da cutar kansa, sun bani wata guda kafin in bar duniya, mahaifinki ya bani shawarar muje hutu don hankalina ya kwanta lokacin da zamu dawo in mutu cikin kwanciyar hankali. Babanki bai taba bata mani rai ba, ya nuna mani kauna da kulawa, ki bishi ki faranta masa rai, kiyi mani alkawalin zama yarinyar kirki. Mahaifiyarki Jessica”.

Yarinyar na karanta wasikar sai ta fasa wata kara tace wayyo Allah tana dubawa cikin akwatin sai taga wata wasikar ta buga sai taga mahaifinta ne Moses ya rubuta mata da taken, “abin da ya faru a cikin jirgi”.

Ya rubuta an bamu riga daya mahaifiyarki tace kaga yau saura kwanaki goma in mutu kamar yadda likitoci suka bayyana don haka rayuwa ta bata da wani amfani kai zaka saka rigar tsira don ka rayu ka kula da diyarmu. Da hannu ta kowa na gani ta sa mani rigar muna kukan rabuwa gaf da zata sullube daga hannu na, sai tace kayi hakuri da diyarmu, kar ka fada mata me ya faru a nan kar kuma ka gwada mata wasikar dana rubuta, ka kula da ita, kayi alkawalin haka? Sai nace nayi.

Duk wannan shekarun ina kokarin kiyaye alkawalin dana dauka nata ne, na kuma cika. Na san kin rika abin da kika rika yi ne, bisa rashin sani, don haka na yafe maki amma don Allah ki zama yarinyar kirki a cikin al’umma abin koyi da misali. Mahaifinki Moses.

Tana kawo karshen wasikar sai ta mirgine a some, tana farkawa a kidime ta nufi makabartar da aka rufe mahaifin ta tana tafiya tana na bani na lalace, kaicona da rayuwa ta, tana isa kabarin ta kife a saman kabarin tana kuka.
……………………._________________________________
Kaji dadin labarin nan ? Aika da ra’ayinka a email katsinaoffice@yahoo.com. ko lambar waya ko WhatsApp 07043777779. ko ga jaridar Taskar Labarai dake www.taskarlabarai.com da ‘yar uwarta The Links News dake www.thelinksnews.com. da kuma sauran shafukan sada zumunta na Facebook.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here