NA TAIMAKI SHUGABAN KASA BUHARI DA APC AMMA YANZU INA DANDANA KUDATA

0

NA TAIMAKI SHUGABAN KASA BUHARI DA APC AMMA YANZU INA DANDANA KUDATA

Daga Taskar Labarai

Wani littafi da tsohon ministan shara’a na Nijeriya ya rubuta mai suna da Turanci “Muhammed Bello Adoke Burden of Service”. Labarin rayuwarsa da aikin da yayi ma kasa.

A cikin littafin ya bayyana cewa da yana ministan shara’a babu matsin da bai sha ba na ya bayyana cewa Buhari bai cancanta ba amma yaki mika wuya ga tursasawar, yace ofishin sa, na iya hana shi takara ta amfani da wasu kura-kurai a takardar kammala sakandare din shi, amma bai yi hakan ba.

Yace an kuma matsa mashi ya tono wasu ayyukan Buhari na baya da yana shugaban kasa a soja shi ma yaki yarda yayi hakan, yace an kuma matsa mashi yayi amfani da wasu kalaman tunzura jama’a da yayi ya kai shi kotu a haramta masa takara duk bai yi ba.

Ya kara da cewa da aka fadi zabe da shi aka lallashi Jonathan ya kira Buhari ya taya shi murna, yace hatta mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya kalle shi ido da ido yace shi dan APC ne, saboda yadda yake bada shawarari na gaskiya.

See also  Zamu Kai Ƙara Kotu Kan Magudin Zaɓe Da Akai Mana -- PDP

Yace matar Jonathan ta kalle shi tayi masa walakanci gaban mutane, duk ya shanye. Yace an kai ga hatta shugaban kasa Jonathan ya taba kiran shi a Ofis ya fada masa cewa yana da shakku akan shi amma ya fahimtar dashi.

Yace ‘yan majalisun tarayya suka shirya wata doka ta gadar zare ga shugaban da yaci zabe, har an sa mata hannu ni na hana a mika wa majalisa ita, aka yi ta rikici kowa yasan hakan.

Yace amma saboda naji labarin makircin da ake mani na bar kasar ana gama rantsuwa amma aka sanya hukumar EFCC suka yi mani bita da kulli.

Yace hatta shugaban hukumar Ibrahim Magu ni na sanya aka maida shi EFCC, bayan da ya bar wajen.
Daga baya ‘yan sandan kasa da kasa suka kama Adoke a kasar Dubai kuma suka mika shi ga gwamnatin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here