MAGANIN RAGE DA HANA ZUNUBI

0

Hikaya daga Taskar labarai
MAGANIN RAGE DA HANA ZUNUBI
_______________________________________________
Asalin wannan labarin an buga shi a wani littafin Hausa ne da aka wallafa tun zamanin Turawan mulkin mallaka, koda yake wanda ya rubuta hikayar ya dauko ta ne ya fassara da Hausa daga wani littafin larabci.

Danjuma Katsina ya sake lale shi da saraffa shi dai-dai da zamanin da ake ciki.Yayi amfani da wani kundin bincike da ya taba yi mai suna fasadi a kasar Hausa don kawo wasu sunayen.

A birnin Katsina an yi wani ja’irin mutum mai suna Daudu ana masa lakabi da gobe Allah ke yi, duk Katsina ba wanda ya kai shi badala da ashararanci. Duk wani aikata laifi ya mai da shi kamar cin abinci ga mai jin yunwa, kowa na shakkarsa duk garin saboda tsageranci da rashin kunya. An kama an buga har an sallama masa.

Da an masa nasiha sai ya buga kafa ya shura takalmi yace gobe Allah ke yi.

Wata Rana akan kan sa ya je wajen sarkin Katsina na lokacin, yace yazo ne don neman a taimake shi da maganin hana zunubi wanda kuma zai rage mashi aikata sabo.

Sarkin yace ya dawo gobe, da safe, kashe gari Daudu yazo Sai sarki ya samu wata katuwar kwatarniya ya sanya aka cika ta taf da ruwa, sannan ya kira hauni ya bashi takobi gayawa jini na wuce, ya kalli Daudu yace masa ga hauni nan a bayan ka zaku shiga gari yawo, umurnin da na bashi shi ne in ka kuskura ruwa digo daya ya fado daga kwatarniya nan to ya fille maka kai, hauni da Daudu da sauran jama’a duk suna ji, sarki yace ku tafi, ka dawo mani dashi da ransa ko kawo mani kanshi, muyi masa sallah.

Daudu da hauni suna barin gidan sarki in da suka fara zuwa shi ne matattarar ‘yan daudu, suka iske dogo Ja’e na zaman ajo, ana ta shagali gasu Idi mai gurmi da Dan Ade mai kurtugi ana ta shakiyanci, tantiran ‘yan Daudu sun hadu ana shake aya da ban iska. Kowa idonshi ya dawo kan Daudu da hauni.

Daga nan suka wuce gidan Abu mai jigida Kyan fada a kwana ana yi. Lokacin an yi wasu bakin karuwai da suka shigo gari su talle mai sitiyari suna ta haba haba dasu. ‘Yan duniya hayakin taba ana sheke aya da chashewa, su hashimu direba yana rawar idon sabbin hannun nan wace zai damka ya ajiye Dadaro? Sai ga su Daudu da hauni kallo ya koma sama lafiya?

See also  Darussan Da Na Samu A Shugabanci A NUJ

Daga gidan Mai jigida sai gidan Lawali a lale kati, yan caca sun hadu kala-kala ana yi ana busa hayakin sigari gasu Dogo “hada husuma shine bariki” ana ta raba idanu.

Daga can suka wuce gidan Andurus a rausaya duk yankin ba gidan giyar da ya kai nashi, Inyamuri ne shi ne ya kawo sai da giya cikin birnin Katsina, wajen ‘yan giya sai layi suke da tambele, ana harba kafa da Shakar iska.

Duk wani wuri na tantiranci sai da Daudu da hauni suka je, sannan suka dawo fada can da la’asar sakaliya, ana isowa aka sauke kwatarniya akan daudu sai ya zube kasa, ragajam somamme.

Bai farka ba sai gab da magariba, da ya farka sarki yace yaje yayi wanka aka kai masa abinci yaci hankalin shi ya dawo.
Bayan Isha’i sarki yace a kira shi, da yazo sai sarki yace Daudu ya yawon da kukayi a jiya? Daudu yace, uhm, sarki yace , naji ance kunje wuri kaza da wuri kaza, Daudu yace albaka nasara ban sani ba, yace wuri kaza fa? Yace shi ma ban sani ba, duk inda aka yi ma daudu magana sai yace bai sani ba.

Sarki yace don me? Daudu yace Allah baka nasara hankalina da tunani suna a hauni yana baya na da takobi tsirara an bashi umurnin ya sare ni, in digon ruwan kwartaniyar dake kaina ya fado kasa, don haka ina kiyayewa ya zan tabbatar ruwa bai zuba kasa ba. Sarki yayi murmushi.

Daudu yace Allah baka nasara, na roki maganin rage zunubi amma sai azaba na samu mai makon hakan. Sarki yace ai maganin aka baka a aikace, ka koma rayuwar kamar kana kallon malaikan mutuwa akan ka, da dauko duk darasin daka samu a wadannan awoyin ka canza rayuwar ka dasu kaga ya zasu koma?

Daga ranar Daudu ya zama mutumin kirki, har ma da ya rasu aka dauka waliyi ne, rayuwar shi ta koma daga karatu sai karantarwa sai kuma ibada.
________________________________________________
Kaji dadin labarin nan? Rubuto ra ayin a layin WhatsApp na 07043777779. kuma ka rika ziyartar shafukan Taskar Labarai dake a www.taskarlabarai.com na the links news dake www.thelinksnews.com da bisa sauran shafukan Facebook, Instagram, Twitter, da YouTube..sai wata litinin din zamu kawo maku wani labarin mai darasi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here