YAN BINDIGA SUN KAI MUMMUNAN HARI A WASU KAUYUKAN DAN-MUSA DA SAFANA.

0

‘YAN BINDIGA SUN KAI MUMMUNAN HARI A WASU KAUYUKAN DAN-MUSA DA SAFANA.

A ranar asabar 18-04-2020 da misalin 8:00am na safe wasu gungun ‘Yan bindiga masu tarin yawa, suka yima wasu kauyukan kananan hukumomin Danmusa da Safana dake cikin jihar Katsina, dirar Mikiya.

Kauyukan da abin ya shafa sune; Barza, Kureci, Gurzar kuka, Gurzar gamji, da Makanwaci.

A wannan mummunan harin da suka kai, ‘Yan bindiga sun yi amfani da bindigogi suna bude ma mutane wuta, wasu kuma suna amfani da adduna suna sarar mutane kamar ana yankan kubewa, sannan sun rika kona rubunan hatsi da sauran abin amfani, haka kuma sun sace dabbobi a kauyukan da abin ya shafa.

See also  Zamfara ta rufe makarantu 10 sai abinda hali yayi

Mazauna garuruwan sun tabbatar mana da cewa an kashe mutane fiye da hamsin (50+) domin har zuwa hada rahoton nan ana suna cigaba da tattara gawar-wakin mamatan da abin ya rutsa da su.

Mazauna yankunan sun ce ‘Yan bindiga sun kwashe awa biyar suna tabka ta’asar su ba tare da samun wata tirjiya ba. Amma daga baya an ce jama’an tsaro sun kai masu dauki marar amfani domin lokacin da suka kai daukin har ‘Yan bindiga sun kammala aikin nasu na ta’addanci sun kama hanya sun gudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here