ABIN DA KE DAMUNMU YAFI ANNOBAR CORONAVIRUS~~~ Shehu Dalhatu Tafoki
Mataimakin Kakakin majalissar dokoki ta jihar Katsina Hon. Shehu Dalhatu Tafoki Danmajalissa mai wakiltar karamar hukumar Faskari, ya bayyana wa manema labarai cewa annobar da ke damun su a karamar hukumarsu tafi ta Coronavirus.
Ya bayyana cewa ya zuwa yanzu da yake wannan magana an kashe mutum uku kuma mutum uku suna asibiti banda wadanda suka tafi basu san inda suke ba. Ya kara da cewa mutanensu masu zuwa itace a cikin daji suma an kame su an tafi da su.
Sati biyi da suka wuce a karamar hukumarsa ta Faskari babu ranar da ‘yan ta’addar ba zasu shigo ba suyi banna, ya kara da cewa ana sanar da su halin da ake ciki kuma su sanar da jami’an tsaro su yi magana da su, amma yadda jami’an tsaron ke mayar masu da amsa basu jin dadin abin da jami’an tsaron ke gudanarwa ko kada.
Karamar hukumar Faskari dai daya ce daga cikin kananan hukumomi takwas na jihar Katsina da ke fama da annobar hare-hare daga masu garkuwa da mutane da masu tayar da kayar baya a jihar Katsina.