YAN BINDIGA SUN KAI HARI KAUYEN KANDAWA

0

YAN BINDIGA SUN KAI HARI KAUYEN KANDAWA

A ranar lahadi 19-04-2020 da misalin 02:00 na dare wasu gugun ‘yan bindiga suka kai hari wani kauye mai suna Kandawa dake cikin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Harin yayi sanadiyar mutuwar mutum daya mazaunin kauyen na Kandawa, sannan sun yi awon gaba da babura guda bakwai (7) da suka shiga gidajen mutane suka kwata.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun yi harbe-harbe cikin kauyen ba tare da samun wata tirjiya ko dauki ba daga makwabta ko jami’an tsaro ba, sannan suka sulale abin su.

A wani labarin kuma, wasu da ba a iya tantancewa ba sun tsallaka gidan wani bawan Allah mazaunin kauyen Yandaka dake cikin karamar hukumar Batsari, suka yi mashi dukan kawo wuka, lamarin ya faru ne da misalin 12:00am na ranar lahadi 19-04-2020.

Amma daga bisani an garzaya da shi babbar asibitin Batsari domin ceto rayuwar shi, su kuma maharan tuni suka arce a guje lokacin da jama’a suka farga suka kawo masa dauki, duk da yake maharan sun yi kokarin harba bindiga toka amma bata hana jama’a tabuka irin nasu kokarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here