MUTUWAR MUTANE A KANO: HAWAN JINI, ZULLUMI DA CUTUTTUKA NE.

0

MUTUWAR MUTANE A KANO: HAWAN JINI, ZULLUMI DA CUTUTTUKA NE.

Daga Binciken Musamman na Taskar Labarai

Wani bincike da Jaridar Taskar Labarai tayi ta gano wasu da suka mutu a Kano, sun rasu ne sakamakon cutar hawan jini wanda ake zargin ta samu ne sakamakon zaman gida ba zuwa wajen kasuwanci da gwamnatin jihar ta kuble.

Wasu ‘yan uwan mamatan da jaridar ta zanta dasu sun nuna damuwa wanda ya tado da hawan jini shi ne abin da ya kashe wasu mamatan.

Lamarin kuma yazo da cewa zaman gidan ya kuble duk wata hanyar kudin shiga balle har ayi tunanin zuwa asibiti na gwamnati ko na kudi don haka duk abin da ya taso ana tunanin in kashe kudi ina za samo wasu na sauran bukatu?

Jaridar Taskar Labarai tayi magana da wasu da suka tabbatar mata zullumi da tunanin makomar kasuwancin wasu ya haifar masu da cuta, wasu takai ko abinci basa iya ci.

Wani fa yace mahaifinsa ya rika zullumin cewa tun bayan gobarar kasuwar Kano yake rayuwa akan bashi yanzu kuma wannan bala’i ya kunno kai, zai kara kamowa ruwa tsundum.

Wata mata ta shaida mana cewa ana sanar da kulle Kano, mijinta ya yanke ya fadi bai kara lafiya ba sai dai kabari aka kai shi.

Wasu kuma masu kananan sana’o’i ne, a kasuwanni wadanda jin ba sauran fita ya haifar masu da matsalar da ta kai su lahira. Taskar Labarai ta ga no irin wadannan mutanen sun kai talatin.

Duk zantawa da masu kula makabartun nan tsawon shekaru sun tabbatar, lallai an samu karuwar mutuwa a Kano fiye da a baya tsawon shekaru.

Babu wani tabbacin cewa cutar Coronavirus ce ke wannan kisan don babu wani gwajin kimmiyya da ya tabbatar da hakan.

Har zuwa hada wannan rahoton ba wani bincike da gwamnatin ta fara na mace-macen don gano me ke kawo su.
________________________________________________
Taskar Labarai jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma ta Turancin ta mai suna The links news dake a www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta. Waya ko WhatsApp a 07043777779 da kuma 08088895277

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here