Karayar Arziki: Gidajen Yada Labarai Zasu Tafi Hutun Dole

0

Karayar Arziki: Gidajen Yada Labarai Zasu Tafi Hutun Dole

Biyo bayan halin da Duniya ta shiga ciki na matsin tattalin arziki da annobar Corona da ke addabar Duniya da kasa Najeriya, Kungiyar masu Gidajen yada labarai Talabijin da Rediyo masu zaman kansu sun yanke shawarar dakatar da ayyukan su har sai abinda hali yayi.

Gidajen Talabijin da Rediyo guda 40 wadanda suke da Ma’aikata 40,000 da Jama’a masu sauraren su Milyan 80 ne suka cimma wannan matsaya a karkashin Kungiyar da ke shiyyar Arewacin Najeriya wacce aka kafa ta a shekarar 2014.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da shugaban Kungiyar kuma mamallakin Gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty da Jaridun Voice Of Liberty da Muryar ‘Yanci Ahmad Tijjani Ramalan ya sanya wa hannu kuma aka rarraba ta ga manema Labarai a Abuja.

Sanarwar ta kara da cewar tuni sun rubuta takarda sun aikewa Kungiyar Gwamnonin Arewa da sauran cibiyoyin da suka dace, domin neman tallafi da daukar nauye nauyen shirye shiryen su da bada tallace tallace domin dorewar aikace aikacen su, kuma tun kafin afkuwar iftila’in da ake ciki Kungiyar ta dade da mika koken ta ga gwamnatoci domin a taimaka wajen fitar da A’i daga Rogo.

“Hakika a fili yake an san da irin rawar da kafafofin yada labarai masu zaman kansu suka taka ta fuskar ilimantar da Jama’a, taimakon Gwamnati wajen yada aikace aikacen ta, da taimakawa wajen yaki da Ta’addanci da sauran ayyukan assha, hakazalika da bada muhimmiyar gudummuwa wajen ilimantar da Jama’a akan illar cutar Corona.

“Babu mai shakka akan irin rawa da gudummuwa da kafafofin yada labarai masu zaman kansu suke bayarwa ta fuskar ilimantarwa da wayar da kan Jama’a, hakanan da taimakawa Gwamnati wajen yada manufofinta da aikace aikacen ta ga Jama’a

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here