BALA ABU MUSAWA YAYI RABON KAYAN AZUMI

0
334

BALA ABU MUSAWA YAYI RABON KAYAN AZUMI
……….daga ..sanata Mandiya,Malik Anas da Abdullahi Aliyu.
Daga taskar labarai
Sanata Bello mandiya, akanta janar na jaha.malik Anas.da kuma wani matashin Dan siyasa mai suna Abdullahi Aliyu sun tara kaya da kudi na azumi da aka raba a karamar hukumar musawa ga Al umma.
Anyi taron rabar da kayan ne kamar yadda aka Saba duk shekara,sai dai wannan saboda dokar hana yawo ta Sanya anyi taron ne a bisa kaidar da gwamnati ta shimfida.
Jawabin shugaban kwamitin bada kudin, Alh Bala Abu Musawa, wanda shi ne mataimakin Shugaban jam’iyar APC Na shiyyar Funtua, ya gabatar ya bayyana cewa su dama a shiyyar Funtua in ana gobe azumi kusan duk dan shiyyar ya san zai samu taimako daga mutanen da ya zaba, inda za a yi gangami, amma bana saboda halin da ake ciki sai aka tattara shugabanin jam’iyya kawai domin su isar da sakon ga sauran al’umma.

Ya bayyana cewa Sanata Mandiya ya bayar da Naira miliyan talatin, inda ya ware naira miliyan sha shidda ga shugabanin jam’iyya, an ba shugabannin jam’iyya na mazabu naira dubu dari, sai na karamara hukuma naira dubu dari biyu sai shugabanin jam’iyya na jiha ya basu dubu dari biyar.

Abu na biyu ya bayyana cewa su a karamar hukumar Musawa ‘yan gata ne a fannin siyasa, inda yace a da ana masu dariya cewar bama ba Abu Ibrahim an ga yadda zasu kare, sai Allah ya kawo masu dauki wasu daga cikin yaransa suka zo suka ce sun hutar da Abu Ibrahim, daga cikin wadanda suka taimaka masu akwai Akawunta na jiha Malik Anas wanda ya basu buhun gero dari sikari buhu dari domin a tallafawa mutanen da ke gidan Bala a siyasa.

Sai wani matashin yaro dan siyasa Abdullahi Aliyu wanda shima dan Musawa ne ya bada kayan abinci da suka kai kimanin miliyan goma sha biyu da dubu dari biyar shi kadai.

Da yake jawabi a wajen Alh Bala Abu Musawa, yace badan Allah ya kaddari ‘bullar Annoba ta Coronavirus ba, da yanzu Sanata ya fara gudanar da aiyukan ruwan sha a dukkanin kananan hukumomi sha daya na shiyyar Funtua, wanda yayi kokarin saka su Cikin kasafin kudin na wannan shekarar ta 2020.

Haka nan za’a gina Manyan Dam-Dam a kananan hukumomin shiyyar Funtua, domin gudanar da noman rani ta hanyar dogaro da kai.

.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here