NI NA KASHE MATATA

0

NI NA KASHE MATATA.
________________________________________________
Wannan labarin an tsakuro shi ne daga wani bidiyo da aka yi,na ilmantarwa da shakatawa. Danjuma Katsina ya sake tsaro shi dai-dai da karatun yanzu.
_______________________________________________
A kasar Oman wani mutum mai suna Salim yayi auren kauna da soyayya da matarsa mai suna Hajara suna zaune cikin kaunar juna, har Allah yayi masu haihuwa ta da mamiji mai suna Abdullahi.

Matar da mijin duk suna aikin gwamnati, dan nasu kuma yana gaf da gama firamare zuwa sakandare. Wata rana sai aka kawo sabuwar ma’aikaciya a inda Salim ke aiki, tana ganin Salim taji tana sonshi. Sai ta shiga yi masa fari da kwarkwasa ba a Dade ba, sai ya kamu suka fara hira har soyayya ta shiga. Kama kama sai maganar aure.sai ya fara canza wa matarshi.

Wata rana daga wajen aiki, Hajara taje asibiti aka gwada akan wasu cuta dake damunta a mahaifa, bayan an bata sakamakon gwajin tana son magana da mijinta amma a lokacin ya fara canza mata, sai ta danne, tana jiran lokacin da ya dace suyi magana.

Ranar nan sai Salim ya ce wa matarsa, gaskiya na hadu da wata da ke son in aura ta, don haka ina son mu rabu dake ga takarda rubuta mani sharuddan rabuwarmu.

Matar kwalla ta cika mata idanu, tace sharadi na daya ne, in ka amince zamu rabu cikin mutunci, yace minene? Tace Dan mu Abdullahi nan sati daya zasu fara jarabawa kuma zasu dau sati uku sunayi jarabawar zata fito cikin sati hudu.

Bani son abin da zai daga masa hankali, musamman a yanzu, don haka ina son kar mu rabu sai nan da wata daya, yace na amince.

Tace sharadi na biyu a cikin kwanakin talatin mu rika rayuwa kamar watan mu na farko da muna ango da amarya, muci tare musha tare mu yi wasanni ka dawo gida da wuri, tace wannan zai ba Ddan mu kwanciyar hankalin karatun shi da jarabawar da zai yi ta kammala firamare da shiga sakandare, yace ya amince tace ta gode.

Ranar farko Abdullahi yaga mahaifin sa ya dawo da wuri haba yayi ta tsalle yana murna yaga sun koma cin abinci su uku tare murna ta kara rufe shi.

Wata Rana yaga mahaifin shi ya goyo mahaifiyarsa suna wasa ya daka tsallen farin ciki,cikin kwanaki kadan sai shakuwa ta dawo a tsakanin su, daga nan sai ya fara shawarar ya canza tunanin shi amma yaki shaida mata.

A ranar da wa’adin kwanakin ya cika,ya bar gida bai fadawa matarsa ba,cewa ya canza shawara ba zasu rabu ba.

Yaje wajen aiki ya shaida wa budurwar sa cewa ya canza shawara ba zai aure ta ba, zai ci gaba da zama da matarsa. Ko don su kula da dan su, kuma matarshi tana sonsa ba dalilin da zai rabu da ita.

Daga wajen aiki ya zarce wani shagon sayen kayan kyauta da kawa ya sawo don yi wa matarshi ba zata.
Ya na zuwa gida ya iske dan shi a falo yana kallo da takardar jarabawar shi da gama makaranta yana ta murna ya canye komai, ya tambaye shi ina mamars yaron yace tana sama tana barci kuma tace kada wanda ya tada ta sai in kai ne kazo, yace taga takarduna har kukan murna tayi.

Baban yace to bari in je in tado ta, yana shiga dakin sai ya iske ta kwance gefen ta ga takardun asibiti, ga kuma wata takarda da ta rubuta.

Ashe dama an gwada ta tana da cutar kansa, kuma zata kashe ta cikin wani lokaci kanka ne, don haka duk zaman da ake karfin hali take, a ranar taji ciwon ya fi karfin ta, taje asibiti aka shaida mata cewa yanzu zai kwantar da ita. Ta ga kuma yau zasu rabu da mijinta in sun rabu wa zai kula da ita?
Tana komowa gida sai ta rubuta ga yar takarda.

“Salam.. ina son ka ka kula da dan mu Abdullahi Sai mun hadu a Darussalam, ta sha guba ta mutu.”

Salim na gama bin takardun dake gabanta. Sai ya fadi kasa somamme ya na fadin na kashe matata.!!!
_______________________________________________
Kaji dadin labarin nan? Rika ziyartar shafukan Taskar Labarai dake a www.taskarlabarai.com da kuma Facebook da sauran shafukan sada zumunta. Da shafin The links news dake a www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta. Duk ra’ayi ko labari aiko ga 07043777779.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here