MATSALAR RUFE KATSINA: TAKARDUN IZNI YAWO SUN YI YAWA.

0
238

MATSALAR RUFE KATSINA: TAKARDUN IZNI YAWO SUN YI YAWA..
………….Ana kamun kafa don a samu
,,,,,,,,,,,,,,, jami an tsaro sun fara koke akai.

Daga Taskar Labarai

Wasu masu tsare hanyoyi don tabbatar da dokar zama gida da gwamnatin Katsina ta sanya kuma aka mai da ta doka, sun ce takardun iznin yawo wadanda ake kira da pass permit sun yi yawa.Har basu iya gane ta gaskiyar da kuma ta bogi.

Binciken da Taskar Labarai tayi ta gano abin ba tsari wanda mai makon abar babban kwamiti shi ne wanda zai iya bada irin wannan iznin kuma ya zama guda daya iri daya yadda jami’an tsaro zasu iya aiki a tsanake.

Lamarin sai ya zama ba hakan ba, yace babban kwamitin ya bada nashi, ofishin sakataren gwamnatin jiha ma yayi nashi, ma aikatar lafiya ma sunyi nasu , sai kuma wani kwamiti da aka ce wai na wayar da kan jama ‘a ne shima yayi nashi.

Dukkaninsu an basu iznin cewa in suka nuna maka ka kyale su wuce, kuma duk hudun sun sha bamban a tsari da bayani da kuma wadanda suka sanya masu hannu.

Binciken ya gano har wani karami akawo na saka wa aljifu, da an tsaida mutum sai ciro ya nuna, kuma ya wuce abinshi yana hura hanci.

Binciken ya gano duk masu samun irin wadannan iznin zirga-zirgar wasu basa da alaka da wani aikin musamman an basu ne kawai don sun san wani sai a basu lasisiin watayawa.

Binciken mu ya gano, Duk wadanda babban kwamitin zai ba katin iznin gaskiya sun cancanta kuma suna wani aiki da ya shafi yawo da zirga-zirga haka ma wanda ofishin sakataren gwamnatin jiha ya baiwa.

Amma na ma’aikatar lafiya, duk yan alfarma suke watayawa dasu, jami an tsaro sun taba tsare wani mai walda da katin izni na ma aikatan lafiya.mafi munin shi ne wanda kwamitin da ake kira na da kan jama’a ke badawa. Wannan ana rabar da shi kamar yadda ake raba gayyatar daurin aure.

Binciken mu ya tabbatar da mafi yawa wadanda bai dace ba suna amfani da wannan iznin ne.
Wani jami’in tsaro ya tabbatar mana da cewa, sun tsare wani da bai dace da katin ba, ya fada masu cewa ya samo shi ne ta hanyar wani abokinshi dake aikatau a gidan daya da ga cikin ‘yan kwamitin.

Wani lamarin sai kaga mutum ya ba matarsa, da kanen ta da abokin dan shi, wani jami’in tsaro ya tabbatar mana da cewa sun tsare wata mota yara uku ke cikin ta kowa na rataye da tag din shi.

Jami’an tsaron sun koka mana cewa, a doka dole su bi duk yadda aka basu umurni, don haka duk mai tag sai dai su daga mashi hannu. “amma rikita mu bamu san na karya da gaskiya ba.

Wannan korafin, jami’an tsaron sun yi shi a wani zama kwamitin yaki da cutar da aka yi a ranar litinin data gabata.
Wani babban jami’in ‘yan sanda ya shaida wa kwamitin cewa, an yi katin izni daban-daban kuma an bamu umurnin duk mu kyale su ba a haka?

Don haka, dokar na aiki ga talaka ka’in da na’in masu uwa a gindin murhu kuma zasu iya samun katin watayawa.
Ra ayoyi sun ce ya kamata a maida katin waje daya a soke wadanda aka bada a sake lalen wadand ya kamata a baiwa a gaba.don kiyaye dokar.
_______________________________________________
Taskar labarai jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo www.taskarlabarai.com tana bisa duk shafukan sada zumunta tana da ‘yar uwa ta Turanci mai suna The Links News dake a www.thelinksnews.com da sauran turakar sada zumunta, duk wani sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here