GIDAN MUTUWA

0

Gidan Mutuwa (HOUSE OF DEATH)

Daga Bin Uthman
Daga shafin Zuma times hausa

Wannan gidan da kuke gani a hoto ana kiran gidan da suna “HOUSE OF DEATH” Ma’ana “Gidan mutuwa”, yana wani gari ne mai suna;”Amaigbo Umu-Anu” acikin jihar Imo.

Mutanen ƙauyen basu san wanda ya gina gidan ba, haka kuma basu san mai rayuwa acikin gidan ba, sannan dare nayi za’aga hasken wutan Nepa ta ko’ina duk da cewa babu wata wayan wuta data sauka zuwa cikin gidan, haka ma ba’ajin wani ƙara na generator.

Abinda yafi bada tsoro shine, babu wata ƙofa ta shiga gidan balle gate, duka gidan yana zagaye ne da katanga.

A shekarar 2012 wani matashi mai suna Ebuka Ikechwu yayi yunƙurin sanin menene ke rayuwa acikin gidan, nan take yayi tsalle ya haura katangar gidan, Ganin shi (yaron) da ba’a sake yi ba kenan har yau ɗinnan.

Haka koda tsuntsuwa batabi ta saman gidan. A shekarar 2010 hukumar sauka da tashin jiragen sama ta jihar Imo mai suna “Imo State aviation center”, ta haramtawa jirage bi ta saman gidan.

See also  HATTARA DAI HUKUMAR KAROTA TA JIHAR KANO

Idan kuka lura dakyau zakuga kaya/tufafi an shanya su, wadannan kayan/tufafi suna canza kala lokaci bayan lokaci.

An tabbatar cewa a shekarar 2005 an hangi wata mata mai ɗauke da juna biyu a gefen taga (window) tana kuka fuskarta da jikinta duk jini, daga ƙarshe ta kulle tagan/hundon tun ranan ba’asan yadda ƙarke ba.

Haka ma a shekarar 2018 wasu yara suna ƙwallo/tamaula sai ta faɗa gidan, nan danan aka bugo ƙwallon daga cikin gidan ta dawo musu, shi kuma yaron daya buga ƙwallon ta faɗa gidan a wannan ranan da tsakar dare ya mutu. Kafin ya mutu iyayen yaron sukace sunji an kwankwasa musu ƙofa sau uku sai sukaji murya akace musu yaron ake buƙata.

Wannan gidan (HOUSE OF DEATH) yana Amaigbo a Umu-Anu kusada school of health Imo State.
©Zuma Times Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here