YA BADA KYAUTAR KATAFAREN GININ SHI DON MASU CUTAR CORONAVIRUS

0

YA BADA KYAUTAR KATAFAREN GININ SHI DON MASU CUTAR CORONAVIRUS

Daga Taskar Labarai

Alhaji Hamisu Gambo tsohon shugaban karamar hukumar Katsina, tsohon dan majalisar tarayya a jam’iyyar APP. Kuma tsohon dan takarar sanata a zaben 2019 a jam’iyyar PDP. Ya bayar da katafaren ginin shi dake lambun Danlawal don mayar da shi wajen kula da masu fama da cutar Coronavirus.

Ginin wanda ke cikin lambuna Kofar Sauri wanda aka tsara shi don gina asibiti da makarantar koyon jinya, yana a yanayi dai-dai na kula da marasa lafiyar da ake tsoron kar a dauka.

Katafaren gine ne, wanda har da ofishin ‘yansanda ke ciki wanda ke aiki don mutanen unguwar, ga shuke-shuken itace wanda zai samar da iska mai inganci ga maras lafiya.

Alhaji Hamisu Gambo wanda kuma shi ne Danlawan Katsina, Dan kasuwa ne mai taimakon jama’a Wanda saukin kanshi da allherin shi ba boyayye bane a Katsina.

Yace halin da ake ciki na kowa ya bada gudummuwar sa ne, ta yadda zai iya don haka, ya sadaukar da ginin wanda kudin shi da aikin da aka yi da shi ya fi naira miliyan dari uku, yace yana son jam’in yaki da wannan cuta su zo su duba shi suga ya zasu iya amfani da shi.

Danlawan na Katsina, yace ya isar da sakon ga wasu manyan ‘yan kwamitin kuma yana sauraren amsa daga wajensu.

Hukumomi dai na kira ga masu hannu da shuni su ajiye banbancin kome a gefe daya su zo a hada karfi don tunkarar wannan annoba.

Ko a satin da ya wuce, sakataren gwamnatin tarayya yayi kira ga masu hannu da shuni su sadaukar da Aron wuraren su da ba su amfani da shi ga hukumar NCDC don su yi amfani dashi wajen killace marasa lafiya.

Wannan kishi da Danlawan ya gwada abin a yaba ne, kuma a karba don aiki dashi.
________________________________________________
Taskar labarai jarida ce mai zaman kanta dake a www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta na yanar gizo. Tana da ‘yar uwa ta Turanci mai suna www.thelinksnews.com duk Kira ga 08088895277, WhatsApp 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here