DARASI DAGA RAYUWAR BABBAN TSUNTSU MAIKI

0

DARASI DAGA RAYUWAR BABBAN TSUNTSU MAIKI

Hikaya daga Taskar Labarai

mun tsakuro labarin ne daga wani bidiyo da aka yi na tsuntsu nan mai suna maiki, ko mikiya. Danjuma Katsina ya gyara sake rubuta shi daidai isar da sakon masu karatu.
________________________________________________

Daya daga cikin tsuntsaye masu ban mamaki akwai maiki yana tashi sama yana iya bin dabbar kasa da gudu daga sama ya kamata, yana iya hango kifi na a ruwa ya wo suka ya dauko shi.

Maiki na iya rayuwa ko arba’in ko tamanin a duniya. Sai Wanda ya zabar wa kansa. Maiki na ji da karfi da isa har tsawo shekaru talatin zuwa arba’in, amma da ya kai wadannan shekarun jikin sa zai yi nauyi, kofaton kafar sa zasu dakushe, fukafukansa zasu yi tsini bai iya tashi, tsinin bakin sa zai koke.

In ya zama haka abu biyu ya rage masa na daya ya samu wata saura yunwa ta kama shi ta sakar masa cuta ya mutu.
Ko kuma ya tashi sama yaje wata sheka kusa da wani Dutsi, a nan zai rika tsigar gashin jikinshi har sai ya cire shi baki daya don sabo ya fito.

Bayan ya tsige gashin jikan shi, sai kuma ya rika karta bakin sa a Dutsi har sai tsohon zunbutu bakin shi ya cire ya koma wawulo. Daga nan sai ya fara karta farce kafafuwansa har sai ya cizge duk tsaffin don sabbi su fito.

See also  akbar...wannan shine ramin kabarin da aka rufe mahaifiyar sarki Kano da Dan uwansa sarkin bichi.

Zai rika wannan cikin zafi da jin ciwo amma ya san wannan shi ne mafitar shi na samun sabuwar rayuwa.

Daga nan zai jira har sai ya tabbatar da duk sabbin sun fito, haka zai zauna cikin jinya da yunwa a hankali sabon gashi zai fito, sabbin faratan kafa zasu fito, sabon zunbutun baki zai fito.

Daga nan sai ya girgije ya fito da sabon karfi. In ya fara sabuwar rayuwa zai iya wasu shekaru arba’in a duniya kafin yayi mutuwa cikin natsuwa.

Darasi daga rayuwar maiki shi ne in har kana son ka dade kana jan zaren ka sai ka tafi da zamani kuma ka rika tafiya da canji.

Duk lokacin da zamani yazo kayi ilminsa ka kuma tafi da tare da shi duk lokacin da ka bar kanka da tsohon tsari tsohon alkawali to tabbas za a rika yi babu kai zaka zama tsohon yayi kana ji kana gani zaka zama gawa mai rai.
________________________________________________

Kaji dadin labarin nan? To ka tarbe mu sati mai zuwa kuma ka rika bin shafukan Taskar Labarai dake www.taskarlabarai.com da kuma the links news dake www.thelinksnews.com. Sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here