SUN KAI HARI HAR SUN YI KISA A YANKIN BATSARI.
Daga jaridar taskar labarai
Wasu mahara dauke da bindigogi sun kai hari kauyen Saki jiki (Bakin gulbi) wanda bai fi nisan 5km ba daga Batsari, kauyen na cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Sun kai harin ne da misalin karfe 12:50am na daren litanin 04-05-2020, harin yayi sanadiyar rasuwar wani mutum mai suna Mallam Lawal Mai Nama Wanda yayi kokarin taimaka ma wanda suka je domin yin garkuwa da shi, sun bindige shi (Mallam Lawal Mai Nama) har lahira, sannan wani shi ma suna Abdulhamida shima sun harbe shi ga ciki amma an garzaya da shi babbar asibitin Batsari daga bisani kuma aka wuce da shi asibitin Katsina domin samun nasarar ceto rayuwar shi.
Sannan sun yi nasarar yin garkuwa da mutumin da suka je domin shi mai suna Mallam Ayuba Jikan Delu, wanda daman mazaunin kauyen ne amma kwanaki baya da matsalar ‘yan bindiga tayi tsanani ya koma Katsina da zama sai a baya-bayan nan da ya ga lamarin yayi sauki ya dawo gida domin cigaba da harkokin shi kamar yadda aka saba, sai gashi Kuma sun yo waiwai da baya sun yi awon gaba dashi.
________________________________________________
Don labarai masu zafi jeka shafukan taskar labarai da the links news a www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com kana da labarin da kake son a bincika aika sako ga 07043777779 ko Kira. Zamu kiyaye sirrinka.ba Wanda zai San wa ya fada mana.