YAN TA ADDA SUN KAI HARI GARURUWA UKU DARE DAYA A BATSARI JAHAR

0

YAN TA ADDA SUN KAI HARI GARURUWA UKU DARE DAYA A BATSARI JAHAR KATSINA
…..sun kashe wasu, wasu suna asibiti
daga taskar labarai

Da misalin karfe 08:30pm na ranar juma’a 08-05-2020 wani ayarin ‘yan bindiga suka mamaye Ruma Tsohon gari da Ruma Sabon gari, da isar su kawai sai suka kama harbi ba tsats-tsautawa, jama’a kuwa duk suka rude domin lokacin wasu na sallar isha wasu kuma sun kammala. Maza da Mata da yara kanana kowa na gudun neman mafaka.
A cikin wannan yanayi ne suka kashe mutum biyu; Hamza mai Nama da Idris Ididda, shi Hamza sun bindige shi ne lokacin da yake gudun ceton rai, shi kuma Ididda sun harbe shi ne lokacin da yake kokarin sake wuri daga inda yake boye a wajen garin kusa da dutsin tandama. Sannan mutum biyu sun samu munanan raunuka sakamakon harbin da suka yi masu, watau Muhammadu Sani da Muntari Yunusa, dukkansu suna babbar asibitin Batsari domin ceto rayuwar su.
A Ruma tsohon gari sun bi gida gida suna neman dabbobi amma basu samu ba domin duk mutane sun riga sun kai su mabuya, har ma wani mazaunin gari dake labe yaji maharan na kokawa suna cewa haka kawai aka jawo mu garin nan ashe ba wata dukiya ke akwai ba. Ana cikin haka sai ga jirgin jami’an tsaro, wannan ne yasa duk suka shige cikin masallaci suka labe wasu kuma suka fake suka daina harbi, wani mazaunin garin da bai samu gudu ba yana cikin masallacin ya labtawa kansa duk shimfidun masallacin yaji su suna cewa, wallahi jirgi mu boye, can sai aka kira daya daga cikin su ya daga waya yana cewa saje lafiya lau muke aiki yana yin kyau. Da kura ta nutsa girgi ya gama yan zagaye zagayen sa ya tafi Kuma sai suka fito suka cigaba da shekar da harsashe.
A Sabon garin Ruma kuwa aikin duk daya ne domin sun bi gidajen mutane sun sace suturu, kayan abinci wayoyi (cellphone) da kudi. Haka dai suka ci karen su babu babbaka tun karfe 08:30 har ya zuwa karfe 12:00am suka lailayi kaya jama’a suka yi yamma,ance sunyi nasarar samun shanu hudu.

Bayan Ruma, wasu gungun yan bindaga sunkai hari kauyen Kuka ukku can ma sunyi harbe-harbe kuma sun sace shanu da tumaki da dama, amma sunyi arangama da jami’an tsaro, anyi ta jin karar harbe harbe.
sunyi masayar wuta da jami’an tsaro sosai, amma duk da haka sai da sukayi nasarar tsira da dabbobin da suka sata. A wannan artabu yan bindigar sun harbi mutum daya mazaunin kauyen mai suna Mubarak Sani, sannan sunyi wa Hamisu Ibrahim dukan kawo wuka, dukkan su suna asibitin Batsari suna jinya.

Sai kuma wani kauye mai suna Chediya, inda suka sato garken shanu da tumaki kuma sun bindige wani matashi mai suna Lawal.
Sai dai jama’a na tsegumin rashin samun dauki daga jami’an tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here