YAN BINDIGA SUN KAI HARI MAI-DORIYA DA KIMBITSAWA.

0

YAN BINDIGA SUN KAI HARI MAI-DORIYA DA KIMBITSAWA.
Daga jaridar taskar labarai

A daren ranar asabar 09-05-2020 da misalin karfe 11:00pm na dare ‘yan bindiga dauke da miyagun makamai suka mamaye kauyen Mai-Doriya dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Da isar su kauyen sai kawai suka kama harba bindigogi daga duk bangarorin kauyen, sannan suka shiga gaidajen mutane suna yi masu binciken kwakwab.
Duk inda suka samu wani abun amfani sai su dauke. Sun sace kudi, suturu, wayar hannu da dabbobi masu yawa da bamu iya tantance adadin su ba.
Bugu da kari sunyi ma mata da dama dukan tsiya kuma ana zargin sunyi ma wasu fyade, inda takai ga da dama sunje asibitin don a duba lafiyar su.
‘Yan bindiga sun kwashe awanni hudu cikin kauyen (11:00pm-3:00am) suna tabaka ta’asa ba tare da samun ko wace irin tirjiya ba, sai da suka gama abinda ya kawo su, suka fice daga garin don radin kansu.
A waje daya kuma wani ayarin na Yan bindiga sunkai hari kauyen Kimbitsawa, ita ma cikin yankin karamar hukumar Batsari. Sunyi harbe-harbe kuma sun sace shanu da tumaki masu yawa.
Kalli hotunan gari da aka kaima Hari, tare da labarin a shafin taskar labarai na yanar gizo ko na Facebook.da Da sauran turakar yanar gizo na jaridar.
____________________________________________
Taskar labarai da The links news jaridu ne dake bisa yanar gizo suna karkashin matasa media links nig Ltd .suna a www.taskarlabarai.com da kuma www.taskarlabarai.com duk sako a aiko ga 07043777779.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here