SHAN GIYAR BERA

0

SHAN GIYAR BERA.

Hikaya Daga Taskar Labarai
________________________________________________
Wannan labarin tsohuwar karin magana ce, amma Danjuma Katsina ya kawo labarin dalilin da ake kiran karin maganar, asalinta da darasin dake ciki abin koyi da dauka ga mai hangen nesa. Asha karatu lafiya.
________________________________________________
Wani bera ne, yana cikin rami abin duniya ya ishe shi, fargaba, damuwa, da zullumi na rayuwar yau da gobe duk sun ishe shi.
Sai ya fito daga ramin shi, yana yawo, har ya isa madafin dake cikin gidan, a nan yaci karo da wata kwalbar giya, sai ya fara sha ya kwankwada yayi tatul.

Ya tafo yana tangadi, sai ya iske wata mage, ta ci ta koshi tana barci ga gashin bakin nan nata yana motsawa in tayi numfashi.

Beren nan cikin buguwar giya, sai yaje gashin bakin magen nan yace ke tashi mutunniyar banza, ya dangwarar mata tsakiyar kai yace dake nake, Mage ta mike, cikin mamaki ta kalli beran nan, ta kura masa ido cikin mamaki, ya dube ta ido da ido yace eh dake nake kuma nine bera, ehe sai me! Yace duk abin da kike takama dashi ni ma ina ji dashi yau.

Beran nan, ya tangaza yaje har gabanta ya sanya hannaye ya bangaji gaban ta, yace ashe matsoraciyar banza ce hakan nan ake tsoron ki a wofi.

Magen nan ta lura beran nan baya cikin hayyacin shi, kuma ita yanzu bata jin yunwa, ko ta canye shi ba wani gardi da zai mata a baki, kuma duk abin da zatayi masa a yanzu ba zata more mashi ba, don baya cikin hayyacinshi. Sai kawai ta yanke shawarar ta kyale shi.

Beran nan ya gama soki burutsun shi, ya tazgada cikin tambele da layi ya fada ramin shi, yana ganin yaci lalai.
Magen nan tayi lamo beran nan giya ta sake shi, ya manta da abin da yayi, duniya ta zama sabuwa yana holewar sa da jin dadin shi.

Wata rana yana cikin cin ganiyar shi, sai tayi wuf ta cafke shi.
Wannan shi ne dalilin da ya sa ake cewa, “za a sake hadewa shan giyar bera”
_______________________________________________
Kaji dadin labarin nan? Rika ziyartar shafukan jaridar Taskar Labarai dake www.taskarlabarai.com da Facebook da kuma shafin The links news dake www.thelinksnews.com da Facebook duk wani Karin bayani aika da sako ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here