YAN BINDIGA SUN KAI KARIN HARE-HAREN A KAUYUKAN BATSARI DA SAFANA.

0

‘YAN BINDIGA SUN KAI KARIN HARE-HAREN A KAUYUKAN BATSARI DA SAFANA.

Data Taskar Labarai

A ranar litanin 11-05-2020 da misalin karfe 8:30pm, ‘yan bindiga sun kai hari Wagini dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Yayin harin nasu sun yi harbe-harbe sannan sun fasa shaguna, sun sace kayan da suka taras da suka hada da kayan tireda, da wayoyi hannu da kudi masu yawa. Da yake ‘yan bindiga sun fito da yawa sosai, sai wasu suka afka kauyukan Hayin Nuhu, Sabon Gari da Bukarawa cikin yankin karamar hukumar Safana.

A Hayin Nuhu sun sace shanu, tumaki, awaki da baburan hawa, sannan sun kashe mutum daya mai suna Munzila. A Sabon Gari kuwa sun harbi mutum daya mai suna Sule Bala SB, sannan sun sace dabbobi masu yawa. A Bukarawa ma sun sace dabbobi masu yawa kuma sun yi harbe harbe-harbe kamar a fagen yaki.

See also  BARAYIN SHANU SUN SHIGA GARIN GIZO

Haka kuma duk cikin daren wani ayari na ‘yan bindaga sun afka ma kauyen Yandaka da karfe 10:30pm, inda suka balle shaguna suka sace kayayyakin da suka taras, sannan sun yi awon gaba da garken awaki, tumaki da shanun jama’a, sun yi kokarin tafiya da wasu ‘yan mata amma daga bisani Allah ya ceto su.

A wani labarin kuma ‘yan bindaga sun kai hari kauyen Kurna dake cikin yankin karamar hukumar Batsari, sun kai harin ne ranar lahadi 10-052020, inda suka yi ta harbe-harbe kamar yadda suka saba, sun harbi mutum daya mai suna Mallam Ibrahim wanda shi ne chairman na ward na jam’iyyar APC (Madogara ward) yanzu haka yana babbar asibitin Batsari yana karbar kulawar Likitoci.

Sannan sun yi awon gaba da tumaki, awaki da shanu da kuma babura kirar boxer guda biyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here