ZUWA GA MAI BA GWAMNAN JIHAR KATSINA SHAWARA KAN TSARO
Ranka ya dade barka da shan ruwa fatan kasha ruwa lafiya, Allah ya amasa mana ibadunmu baki daya.
Ranka ya dade na rubuto maka wannan wasikar ne a matsayi na na da a wajenka kamar yadda ka dauke ne. Ko shakka babu ranar da naga takardar baka wannan matsayi nayi farin ciki kuma na yi bakin ciki. Na yi farin ciki ne domin nasan kana da kwarewa a fannin tsaro, kuma dukkana ayyukan da ka aiwatar a fannin tsaro har ka gama ka cimma nasara. Kwarewarka tasa kusan duk inda kayi aiki ake samun nasara.
Farin ciki na biyu kuma shi ne kasancewarka marubuci a fannin abin da ya shafi tsaro. Littafinka da ka rubuta ka kawo dalilan da ke sa ake fadawa cikin ta’addanci da kuma yadda za a magance su, shi yasa a lokacin na san cewa lallai kakarmu ta yanke saka domin gwamna ya aje kwarya a inda ta dace.
Ranka ya dade kasha shirya taruka kan wannan fanni kuma a cimma nasara. Ranka ya dade in ka tuna wata rana a cikin farko shekarar 2019 ka tafa fada man cewa zaku yi iyakar kokarinku wajen ganin kun kyautatawa Katsina, domin Katsina ta yi maku kome.
Ranka ya dade a iyar sani na da kai kana son cigaban Katsina da mutanenta baki daya, domin duk maganar da zaka yi Katsina ce gabanka. Ranka ya dade kana daga cikin mutanen da kullum nake wa addu’a Allah ya ba nasara a aikinsu.
Ranka ya dade bakin cikin da na yi kuma shi ne zaka yi aiki cikin wasu mutane masu wuyar hali, wadanda suka dauki kome matsayin jari huja. Mutanen da basu damu da wani ya rayu ba su dai kansu kawai suka sani, mutanen da basa amsar shawara sai abin da yayi daidai da bukatunsu. Ranka ya dade kayi hakuri nasan zaka ji maganar wata iri, tabbas haka ne domin kai aiki ka sani ba siyasa ba, duk kuwa da cewa kayi aiki da ‘yan siysar. Na san cewa ba zasu taba barin ka ba kayi tsari irin naka sai sun kawo ma nasu. Wannan ya sa a lokacin na yi bakin ciki da tausaya ma, musamman kan burin da kake son cimma wa na wanzar da zaman lafiya a jihar Katsina.
Daga karshe ina tunatar da kai kamar yadda kullum in muka hadu kake tunatar damu abubuwan da ya kamata mu yi da kuna yadda ya kamata mu zama. Ga dai jihar Katsina nan ta na neman zama wani sansanin yaki, kullum kisa ake ba kakkautawa, Wallahi Ranka ya dade Allah ya sani bani son Allah ya tuhume ka da laifin halin da jihar Katsina ta fada.
Amma ina fatan zaka fito da wani sabon tsari na bayar da shawara wanda a kalla ko da ba a kawar da wannan abu ba amma za a samu sauki, ko shakka babu nasan kasan hanyoyi da yawa da za a bi a magance wannan matsalar duba da dadewarka a wannan aiki, ranka ya dade ka basu shawarar don Allah ko da ba zasu dauka ba, wata rana zata zama hujja a wajenka.
Nagode kwarai
Abdulrahman Aliyu
08036954354