YAN BINDIGA SUN KAI MUMMUNAN HARI A KAUYUKAN SAFANA DA BATSARI.

0

YAN BINDIGA SUN KAI MUMMUNAN HARI A KAUYUKAN SAFANA DA BATSARI.
@ jaridar taskar labarai

Da misalin karfe 10:10pm na ranar talata 12-05-2020 wasu gungun ‘yan bindiga suka afka kauyen Dan Jikko dake cikin yankin karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Kamar yadda mazauna kauyen suka bayyana mamu, ‘yan bindaga sun mamaye kauyen nasu suna harbe-harbe tamkar ana yakin kasa da kasa, sannan suka ware wani bangare na kauyen suka bi gida gida suka tattaro shanu, tumaki da awaki, amma sai suka samu tirjiya daga gare su.

Mazauna kauyen sun yi amfani da bindigogin toka (harba ruga) suna maida martani, haka suka yi ta dauki ba dadi da su tun 10:10pm har zuwa 11:30pm, dalili ke nan da ya hana su tafiya da dabbobin. Sai dai an samu asrar rayukan mutanen kauyen guda biyar sakamakon gumurzun da suka fafata da ‘yan bindigar, wadanda suka rasa rayukan su sune; Jamilu Tijja, Isah Sale, Tijja Kabir, Audu Ila, da Alhaji Bello.

Haka kuma mutane ukku sun samu raunaka samakon harbin da yan bindigar suka yi masu; Musbahu Ma’aru, Yahayya Dawai, da Isiya Garba, dukkan su suna babbar asibitin Batsari jami’an lafiya na duba su.

Haka nan ma a yankin karamar hukumar Batsari, duk a cikin daren na talata 12-05-2020, ‘yan bindiga sun kai hari kauyukan Dullu, Tinya, Maikaren Sharo, Gidan Gusun da Karere.

A kauyen Dullu sun bindige mutum daya ya mutu har lahira, kuma sun yi awon gaba da dabbobi da kayan shaguna da suka fasa.

A Maikaren Sharo ma sun fasa shaguna sun wasashe abin da suka taras kuma sun yi gaba da dabbobi. A Gidan Gusun kuma sun harbi mutum daya, shima yana asibiti yana karbar kulawar Likitoci, sanna sun fasa shaguna sun yi halin nasu. Amma a kauyen Karare yan bindaga basu je da sa’a ba domin jama’a ne suka jajirce suka tarwatsa su.
________________________________________________
Taskar labarai jarida ce dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma yar uwarta turanci dake a www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta. Duk sako a aiko ga 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here