KATSINA CITY NEWS, TA SALLAMI FURSUNONI TA KUMA TAIMAKI MABUKATA ALBARKAR WATAN RAMADAN.

0

KATSINA CITY NEWS, TA SALLAMI FURSUNONI TA KUMA TAIMAKI MABUKATA ALBARKAR WATAN RAMADAN.

Dandalin nan dake musayar ra’ayi da sada zumunta dake bisa shafin Whatsapp mai suna Katsina City News. Yayi wani aiki na biya wa wasu fursunoni tara aka sallame su da kuma bada tallafin abinci ga wasu ‘yan gudun hijira daga Batsari, Safana da kuma Kankara.

Dandalin ya tara kudin nasa ne, Daga membobin da ke cikin shi, Wanda aka bada sanarwar cewa duk mai hali, ya bada akala naira dubu biyu, wanda aka yi ta badawa, har suka taru da yawa.

Shi dai Wanda Dandalin ya tara mutane masu ra’ayin siyasa iri daban-daban, da fahimtar addini kala , da mutane iri-iri duk a cikin sa, ana musayar labarai da muhawara don kawo cigaba a jahar Katsina da kuma kasa.

A shafin dandalin ne, aka bayar da shawarar a kafa gidauniyar a taimaki wasu mabukata. Sannan aka kuma zabi wadanda zasu tafiyar da gidauniyar.

Mutane da yawa sun taimaka cikin su har da mataimakin gwamnan jahar Katsina, Qs Mannir Yakubu da Alhaji Dahiru Usman sarki shugaban kamfani rukunin gidajen mai na DanMarna da Alhaji Idris tune shugaban ma’aikatan jahar katsina, Alhaji Lamis Dikko Ajiyan Katsina , da Hon Bala Banye, da Alhaji Murtala Safana da Alhaji maiwada Dan Malam, Malam Ibrahim Daku. jam’iyyar PDP ta jihar Katsina da kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Katsina Mobile Media Crew katsina da sauransu.

An kafa kwamiti guda uku, kwamitin farko karkashin Barrister Ahmad Danbaba wanda aka baiwa aiki sako wasu fursunoni da akai ma tara ko bashi,Wanda ba suda kudin biya. Na biyu na sayen kayan abinci a karkashin Hajia Murja Saulawa, aka basu aikin sawo kaya da za a rabar. Sai na uku karkashin Dakta Habib na FMC Katsina aka basu aikin tsara rabar da kayan da aka sawo, Dukkaninsu sun yi aikinsu cikin amana da gaskiya.Sai Abdurashid Musa na mobile Media Crew don tattara hotunan aikin.wanda yayi aikin da kishi.

‘Yan gudun hijira daga Safana, Batsari, da Kankara sun amfana daidai abin da aka iya tarawa, aka kuma rabar, sannan sai wasu mabukata dake unguwannin raunana dake Katsina, Wanda suka hada da Masarar kasa, Tudun Matawalle da Kuma Tudun Yan lihida, Suna Daga cikin ungunin da aka tallafa masu.

Wannan shi ne aiki na biyar na taimakon Al’umma da wannan dandali yayi, banda jagorantar addu’ar jiha don samun zaman lafiya da takardar shawara ga gwamnatin Katsina.

Dandalin shi kadai ne, dake tafiyar da zaman sa ba dogara da wata siyasa, akida ko nuna wariya ba da bambanci ba, yana da tsare tsare a gaba na hada kan mutanen Katsina inuwa daya a cigaba bisa tafarkin kowa yana jam’iyyarsa, akidarsa ko fahimtar sa ko tsarin da yake gudanar da rayuwarsa.

Sa hannun
Wanda ya Assasa Dandalilin
Muhammad danjuma.
15/5/2020.

Abdurashid Musa
Mobile Media Crew
May 17/20202.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here