FARGAR JAJI: MARTANI GA DAN MAJALISSA MAI WAKILTAR KARAMAR HUKUMAR RIMI

0

FARGAR JAJI: MARTANI GA DAN MAJALISSA MAI WAKILTAR KARAMAR HUKUMAR RIMI

A kwanan baya ‘yan majalissar dokokin jihar Katsina suka tauna tsakuwa domin ba aya tsoro a game da halin da ake ciki na rashin tsaro a wasu sassan jihar Katsina.

Bayan kammala zaman ne Dan majalissa mai wakiltar karamar hukumar Rimi wanda kuma shi ne shugaban masu rinjaye na majalissar ya yi wani abu da ake cewa ‘Fargar jaji’. Har aka kare zaman Dan majalissar bai ce kome ba, bai kuma bayyana matsayarsa ba ko gudumuwarsa, amma sai ya tara manema labarai a ofishinsa yana masu fargar jaji bayan da ya lura cewa kamar kasuwa ta ci ba shi, kuma na samu riba.

Bababan abin mamaki a cikin bayanan na dan majalissa wanda yake da masaniya sosai kan tsaro, duba da cewa shi tsohon soja ne, shi ne yadda ya koma yana kalubalantar abokanan aikinsa ‘yan majalissu game da bayanan da suka yi. Wanda a majalissar ya kamata a ce ya yi wannan magana ba a idon al’umma ba.

Dan majalissar ya bayyana cewa, wai majalissar suna tare da duk kudurori da kuma muradai na gwamnatin jiha kuma kansu hade yake, amma kuma ya manta abokanan aikinsa irin su Dan majalissar Jibiya da na Kankara sun fito fili suka baranta kansu da gwamnatin APC da sauran duk wasu muradai na wannan gwamnatin musammana abin da ya shafi tsaro.

Ko dai baka san zafi ko radadin da ake ji ba na rasa rayuka da kace ai kanku hade yake kuma baku da wata matsala da gwamnatin, a takaice ka soke waccan maganar da abokan aikinka suka yi.

A bangare mutanen da yake wakilta kuwa, wanda shi ne abin da yafi damuna kasantu wa ta daya daga cikin su. Ya bayyana cewa, ya kai kudurori da yawa da samar da cigaba a karamar hukumar Rimi, tambayar da zan yi a nan ta ina? Ya bayyana cewa ya kai koken gyara hanyoyin cikin garin Rimi, amma kuma a tsawon shekara biyar da ya share ko kwalbati ba a gyara ba.

Ya bayyana cewa ya kai koken gyaran Babbar asibitin Rimi, amma abin takaici ko sirinji ba a kawo ba, ya zuwa wannan rubutun asibitin ma na wani hali na sai da Inalillahi wa’ina ilaihi raji’un, domin karancin kudin gudanar da ita har ta kai ga an sallami duk wani ma’aikacin wucin gadi dake asibitin. In da Hon Korau da gaske yake sai ya dauki masu wucin gadin nan koda mutum biyu ne duba da cewa 10,000 kacal ake biyansu a wata, koda na tsawon shekara guda ya biya za a more shi sosai.

Ya bayyana cewa wai ya kai koken sanya wutar Yanmudi da Siyya, to Hon Korau mun gode, amma wannan koke an kai shi ne tun a zamanin jagorancin Hon Bilya, tare aka kai su da wutar Fardami, wata kila dai kai kayi gam da katar ne kawai. Amma dai mun gode tunda mun san yadda abun yake.

Wani abun dariya shi ne da ka bayyana cewa wai ka kai koken ayi makarantar kwana a Rimi? Shin wace irin makarantar kwanan? Kuma ina koken ya makale? An gina makatantar? Ko kuwa nan ma masu zartarwa ne suka kiya?

Maganar ruwa da kake a Rimi shin ina aikin ya kwana? In ana yi to kayi mana bayanin inda aikin ya tsaya domin mu dai bamu san ta inda aka fara shi ba.

Ni abin da na lufa Fargar Jaji ne kake kawai duba da cewa baka yi wa mazabar ka kome, kuma akwai alkawura da dama kanka shi ya sa kake wanann zagaye-zagqyen domin neman suma da farfaganda, wanda kuma ya zuwa yanzu wuri ya kure maka domin mun san waye kai.

Ranka ya dade, naji kana bayyana cewa wai Buratai ya dawo Katsina saboda magance matsalar tsaro, duk da cewa ba kai ne kayi maganar ba sa ma maganar aka yi a baki, amma ai Buratai dan ya dawo Katsina me zai yi? Kaifa Soja ne, kamata yayi ka fito da hanyoyin da za a magance matslar tsaro a Katsina ta la’akari da gogewar da ka samu. Ba wai ka tsaya kana Farfaganfa da neman suna ba.

Daga karshe ina baka shawara da ka mayar da hankali kan aikinka kayi wakilci na gari wanda Rimi zata dade tana tunawa da kai, kamar yadda magabatanka suka yi, ya zuwa yanzu kai ne mafi koma baya a wadanda suka taba wakiltar karamar hukumar Rimi a matakin jiha, domin babu wani aiki ko kwara daya da za a yi alfahari da shi ta dalilinka, ko hanyar Maje da kake kakarin ka sa an yi ai sharar hanya kawai aka yi, amma a jawabinka sai ka zargi bangaren zartarwa da kin yin aikin yadda ya dace, shin me yasa baka bi kadin aikin ba? Ko shima bin kadin baya daga cikin aikinka?

Na barka lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here