KOYI DA KARE, BIRI DA MAKAUNIYA

0

Hikayar Taskar Labarai

KOYI DA KARE, BIRI DA MAKAUNIYA
________________________________________________
Kamar kowane sati a wannan ma ga wata hikayar mai darasi wadda Danjuma Katsina ya rubuta mana. Labarin na tattare da hikima da tarin ilmi. Asha karatu lafiya.

Allah ya sanya a amfana, ku rika ziyartar shafukan Taskar Labarai na yanar gizo dake a www.taskarlabarai.com da kuma Facebook da shafin The links news dake a www.thelinksnews.com da Facebook
________________________________________________

Wani yaro mai suna Ahmad yayi shekaru yana jinyar mahaifinsa, ranar nan ciwo ya kai gargarar mutuwa mahaifin Ahmad mai suna Salim yace Ahmada cutar nan tawa bata tashi bace, don haka ba zan bar maka komai ba amma zan maka addu’a kuma zan baka shawara guda uku ka rike su a duniya ba zaka tagayyara ba.

Ahmad na kuka yace, baba duk shawarar daka bani ba zan yi wasa da ita ba. Yace da farko duk inda ka samu kanka kai daya kayi koyi da halin biri. In kana karkashin wani kayi koyi da halin kare. In ka samu abu kayi masa cin kwai na makauniya.

Salim yace Biri a daji yana cikin dabbar da bata cikin hatsari, bai da abokin fada, ya nemi abin da zai ci, yayi kwanciyar shi, baya shiga harkar kowa cikin namun daji. Kuma kullum cikin taka tsantsan yake da kula, wurin kwananshi da abin da zai ci. Kar yake kallon kowa amma bai shiga shirgin kowace dabba, don haka da wuya kaga wata dabba ta kashe biri don taci yana da wayon zaman daji kusan yafi duk wata dabbar daji.

Amma kuma biri baya dadin kiwo ga mutum in ya shigo cikin mutane sai an daure shi, sai kuma an sa masa bulala. Don ji yake ba wani abin da ya raba shi da mutum sai magana don haka duk abin da yaga mutum nayi zai kokarin aikata fiye da shi ne, in yaga ana tuka mota zai kokarin gano in da ake ajiye makublin motar yace zai tuka, kome yaga ana yi zai kokarin aikata don haka kullum cikin barnar karambani yake, kuma kullum bugun shi ake. Sai in an daure shi an kuma sanya masa idanu.

Wannan ya sanya ba mai son kiwon biri ya barshi sakaka. babu wanda zai yarda a gaban shi ya aikata wani aiki mai amfani don kar ya kwaikwaya.

Salim yace, shi kuma kare, a daji sakarai ne, kowa sai danne shi ya cinye, amma idan yana wajen mai gidanshi bai san kome ba sai biyayya da sadaukar da kanshi don kare rayuwar mai gidanshi.

Kare bai da aiki sai bin umurnin mai shi. Don haka, maigidanshi zai iya yin komai don kare martaba karenshi, zai ciyar dashi kayan dadi. Kare yana da aminci wajen maigidansa, saboda bai san kanshi ba, maigidansa ya sani.

Salim, yace kaje ka sai kwai ka samu makauniya ka bata kaga ya zata ci sai ka dau darasin dake a ciki.

Ahmad ya samu kwai dafaffe ya samo wata makauniya yace mata ga sadakar kwai dafaffe. Matar nan ta dauka tayi godiya, Ahmad ya koma gefe daya yana jiran yaga me zai faru?

Can sai ga matar nan ta lulaya kwan nan, sannan ta fasa shi a hankali, ta rika cire bawon a tsanake ta shafa shi ta tabbatar da cewa ba wani kwafson bawo a jikinshi sannan ta daye, fatar a hankali ta sake shafar jikin kwan sai ta fara cin kwan cikin natsuwa. Ta cinye tuwon kwan fari, sannan taje ga jan kwallon dake ciki, ta cinye tayi godiya ga Allah.

Ahmad nan ya gane me mahaifin sa ke nufi da duk abin daka samu kayi masa cin kwan makauniya. Watau komai a tsanake a keyi.

Ahmad ya bi duk shawarwarin mahaifin shi ya na kuma jin dadin rayuwarshi.

Sai mun hadu a wani makon insha Allah
_______

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here