NAJERIYA TA KAI DAUKI GA MUTANEN TA MAZAUNA IRAN

0

NAJERIYA TA KAI DAUKI GA MUTANEN TA MAZAUNA IRAN
daga taskar labarai
Gwamnatin Najeriya ta kai daukin kayan abinci ga yan Najeriya mazauna kasar Iran saboda matsalar halin da aka shiga na koronavirus.
An rabar da kaya kamar haka ga kowane mutum daya.
Buhunan shinkafa guda biyu
Robar man gyada guda biyu
Daurin sukari guda biyu
Kwalin macaroni guda daya
Kyalllen Rufa fuska guda hamsin
Safar hannu guda dari
Sinadarin wanke hannu guda daya.
Gasu nan kamar yadda zaku iya gani samfur din a hotunan dake tattare da labarin nan.
Gwamnatin ta Najeriya ta tace yan kasar ta guda ashirin da za su gida. Wanda kowa shune zai biya kudin jirginsa na dawowa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here