AN KAI MU NA NAN HARERE A FASKARI

0

AN KAI MU NA NAN HARERE A FASKARI

daga Awwal Jaula @ taskar labarai

Yan ta’aadda sun ci karansu babu babbaka a wasu garuruwa dake karamar hukumar Faskari jihar Katsina.

28/5/2020 da karfe 11:00 na dare, sun shiga Unguwar Gizo inda suka kashe mutum 13 , suka harbi mutum 7 yanzu haka suna asibiti, sun kuma dauki mace 1 sun tafi da ita. Sun kwashe musu dabbobi gaba daya (Shanu, awaki da Tumaki).

Haka kuma, sun shiga Sabon Layin Galadima sun barke shagunan mutane sun kwashe kayan abinci da kayan masarufi.

Daga nan suka wuce Maigora inda suka barke, shaguna suka kwashe kayan abinci da kayan masarufi kuma sun harbi wani mutum daya.

A garin Mairua kuma sun dauki mutum biyu sun harbi wani yaro.
Mun yi kokarin jin ta bakin jami an tsaro ba muyi nasara ba.
………………………………………………………………………..
Taskar labarai jarida ce dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma yar uwarta ta turanci a www.thelinksnews.com. duk suna bisa shafukan sada zumunta. 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here