Rt. Hon Aminu Bello Masari a Fagen Siyasa: Mun Gani a Kasa ba Labari Ba

0

*Rt. Hon Aminu Bello Masari a Fagen Siyasa: Mun Gani a Kasa ba Labari Ba*

Daukar Nauyi Mun Gani a Kasa ba Labari ba Karkashin Jagarancin Injiniya Surajo Yazid Abukur

“Duk me son ya zama shugaba, to ya zamto bawan waxanda ya ke son shugaban ta, ta haka ne kawai za su kalle shi a matsayin shugaba nagari” ~ (Malam Aminu Kano)

Yakin neman zaben xan takarar gwamnan jihar Katsina a qarqashin inwar jam’iyyar APC Rt. Hon Aminu Bello Masari ya tabbatar da cewa Masari xan siyasa ne da babu irin sa a faxin qasar nan. Masu nazari siyasa sun yi nazarin wasu tarin nasarori da gwamna Aminu Bello Masari ya samu wanda ba’a tava samun wani xan siyasar arewacin Nijeriya da ya same su ba.
Idan za mu iya tunawa vurvushin siyasa ya fara a Arewacin Najeriya ne tun a wuraren shekarar 1940s lokacin da su Sardauna suka qirqiri Jam’iyyar Mutanen Arewa har ya zuwa shekarar 1951 lokacin da jam’iyyar ta koma NPC. Har zuwa zaman Sardauna Firimiyan Arewa daga shekarun 1959 -1966. Duk wani tarihi da gwarazan siyasar lokacin suka kafa, in muka kwatantashi da nasarar da Aminu Bello Masari ya kafa a siyasar sa zamu ga cewa ya masu nisa fintinkau.
A tarihin siyasar Najeriya kaf ba a tava samun wani xan takara da ya nemi muqami karo na biyu ba, kuma ya zaga dukkan qananan hukumomin jihar sa domin yaqin neman zabe, ba tare da samun wani qalubale ba na zagi ko jifa ko kuma kisa ko haxarin mota mai kawo asarar rayuka ba sai Masari.

Rt. Hon Aminu Bello Masari ya zagaya kafatanin qananan hukumomin jihar Katsina kuma ko wace qaramar hukuma ya hau mumbari, ya yi jawabi, ba’a samu qaramar hukuma xaya da aka ce “qarya ne ba” ko “bamu so” ko kuma qoqarin yin wani tunzuri ko tayar da zaune tsaye.
Haka kuma har aka gama rangadin na qanana hukumomi 33 ba a tava samun hadarin mota ba ko wani tukin ganganci da ka iya kaiwa da rasa ko da akuya ce balle xan Adam, yakin neman zabe a ka yi babu ko da gora, balle barandami, adda, takobi ko kaho.
Masari bai musgunawa ‘yan adawa ba, bai tozarta su ba, ya yi masu aiki a garuruwan su kuma yana kawar da kai daga cin mutuncin su ko zagin da suke mashi. Hasali ma hakan ya sanya kusan duk ‘yan adawa suka dawo tafiyarsa, manya daga cikinsu Akwai Dantakarar Jam’iyar PDP da suka kara a zabukkan shekarar 2015 Nashuni, akwai shahararre xan siyasar nan Hon. Abdullahi Umar TATA, Akwai masu adawa daga cikin gida waxanda wannan rubutun ba zai bada damar a fadi kowa ba.

A fagen lafiya da hanyoyi kaxai, ba za a iya kwatanta Masari da gwamnonin farar hular da aka tava yi a Katsina ba, saboda sam ba su kama qafar sa ba wajen ayyukan raya qasa da cigaban al’umma da kuma murqushe adawa baki xaya a jihar Katsina, domin dukkan su ba wanda ba’a jefa ba kuma ba wanda ba a karyata shi gaban sa ba sai Rt. Hon Aminu Bello Masari.
Masari akidarsa a aikace take ba a zuciya ba, domin babu wata qaramar hukuma da ke jihar Katsina da bata amfana da ayyuka sama da guda 60 ba daga Rt. Hon Aminu Bello Masari a vangarorin da suka haxa da Ilimi, Lafiya, Noma, Muhalli, Tsaro, tallafa wa al’umma da dai sauran vangarorin cigaban rayuwa.
Akwai abubuwa da yawa da za a iya kawo wa domin dogaro da su na cewa jihar Katsina bata taba samun gwamna kamar Masari ba.

A fagen Lafiya ya gyara asibitoci da suka haura shekaru arba’in ba a taba yi masu ko da fenti ba. Ya kuma xauki ma’aikatan lafiya da samar da kayan aiki tari guda sannan ya inganta fannin wanda kaf din kananan hukumomin da ke Katsina ba bu qaramar hukumar da bata amfana da wannan ba.

A bangaren Ilimi ya yi ayyuka na gyara Azuzuwa sama da guda 2000 a jihar Katsina, baya ga sababi sama da guda 400 da aka Gina, kama tun daga gina sabbin makarantu da azuzuwa da gyara wa tare da daga darajar wasu makarantun, kara wa malamai girma kan kari da kuma daukar malamai masu tarin yawa, tare da sassauta kuxin rijista a manyan makarantun jihar fiye da kowace jiha da ake da ita a Najeriya.

A bangaren Hanyoyi ba a taba samun wani gwamnan da a kasa da shekaru uku da rabi a Arewacin kasar nan da ya shimfixa hanyoyin da ya shimfixa ba, wanda ba wata qaramar hukuma da bata amfana da akalla hanya guda biyu.

Zamu iya cewa vangaren samar da ayyukan yi da dogaro da kai ba’a samu gwamna a kaf din Arewacin Nijeriya da ya kama kafar sa ba. Haka ma a fannin noma ya raba taki da kayan aikin noma da kuma gyara manyan Dam waxanda suka taimaka wajen havaka harkar noma a jihar Katsina.

A vangaren ruwan sha kowa ya san irin namijin qoqarin da Masari ya ke yi wajen samar da Rijiyoyin Burtsatse sama da guda 2066 a jihar Katsina tare da aikin Dam din Zobe wanda aka yi sama da shekaru 40 ana so a yi shi kuma ba a kammala ba sai yanzu da Rt. Hon Aminu Bello Masari ya xare bisa karagar Mulki, yanzu haka an yi gwaji ruwan sha yazo cikin garin Katsina tun daga Dutsinma, An shimfida Bututun ruwa, kuma ba da dadewa ba cikin garin Katsina dama qauyukan dake hanyar Katsina zuwa Dutsinma za su amfana.

Idan mukace ce zamu tsaya cigaba da zayyano aikin da Rt. Hon Aminu Bello Masari ya yi to za’a iya buga littafi wanda zai xauki tsawon lokaci ana nazarin sa.

Daga Karshe abin da za mu ce shi ne duk mai son zama dan siyasa na gari ya yi koyi da dabi’un Rt. Hon Aminu Bello Masari. Ayi siyasa don cigaban Al’umma, Babu gaba, babu batanchi, babu ta’adanchi, ayi mulki bisa Amana, cancanta da sanin ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here