ANYI GARKUWA DA MATAN AURE A MALLAMAWA, JIBIA LGA.

0

ANYI GARKUWA DA MATAN AURE A MALLAMAWA, JIBIA LGA.
Muhammad Ahmad @ taskar labarai
A ranar laraba 27-05-202 da misalin karfe 12:00am wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne suka afka gidan wani mutum mai suna Mallam Shafi’u dake zaune a kauyen Mallamawa (Sabon Gari) dake cikin yankin karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

Inda suka yi awon gaba da matar shi da kuma matar kanen shi, watau jimla matan aure guda biyu kenan suka yi garkuwa da su.

Jama’a sun fito domin ceto su, ana ta yekuwa amma sai maharan suka yi harbi na ban tsoro, dalilin da yasa kowa ya sha jinin jikin sa gudun abun da ka iya faruwa idan suka matsa, haka dai suka gudu da matan nan har zuwa mafakar su.

Sai dai wata majiya mai tushe na bayyana cewa mutanen garin sun gane wadanda suka yi garkuwa da matan, sun ce wasu Fulani ne dake makwabtaka da kauyen su.

Sannan mazauna kauyen sun koka ganin yadda lamarin ya kasance ba wanda ya kawo masu dauki daga jami’an tsaro duk da kokarin da suka ce sun yi na sanar da jami’an tsaro lokacin da abun ke faruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here