ALLAH YA KUBUTAR DA WATA MATA DA SACE A MUSAWA.

0

“ALLAH YA KUBUTAR DA WATA MATA DA SACE A MUSAWA.
=================================

“Allah ya kubutar wata mata mai suna Hadiza Sale Hassan Musawa da masu Garkuwa da mutane suka dauke ta daga gidan mijinta a garin Musawa ranar 29/04/2020 da misalin karfe daya na dare”.

“Da take ma manema labarai Jawabi bayan kubutar ta “Hadiza Sale Hassan Musawa ta bayyana cewa ranar da barayin suka shigo gidansu sun nemi mijinta tace mijinta baya nan, suka ce ta basu kudi tace masu batada kudin da zata basu saidai dan kunne na zinari dake kunnenta, sai suka mare ta daga karshe dai suka tafi da ita”.

“Hadiza ta cigaba da cewa yadda ta kubuto daga hannun masu Garkuwa da mutane, “tace cikin daren jiya asabar 30/05/2020 Allah ya kawo mata taimako mutane biyu ne suke tsare da ita sai daya daga cikinsu yayi tafiya aka bar mutum daya, shi kuma dayan dake tsare da ita sai bacci ya kama shi mai nauyi”.

“Hadiza ta cigaba da cewa akwai wani bargo da suka bata ta rika rufa dashi, sai tayi hikima ta shimfida bargon kamar tana a ciki kwance Allah yasa ba daure suke da ita ba, dama ta lura da hanyar da suke bi suna fita saita lallaba ta gangaro ta fito sai tayi ta gudu tun karfe goma na dare take gudu cikin daji batasan inda take nufa ba har asuba”.

“Saita hango wani tsauni saita nufo inda tsaunin yake tahau tsaunin ta gangaro ta cigaba da gudu duk inda ta hango alamun wani haske ko gida saita kauce mashi tunda duk cikin dajin gidajen fulanin ne barayi, tana cikin gudu gab da wayewar gari saita iske wata rijiya ana dibar ruwa saita isa gindin rijiyar Allah ya taimake ta hausawa ne ta gaya masu halinda take ciki”.

See also  Direban dake kai fasinja wajen 'yan bindiga don a yi garkuwa da su ya shiga hannu

“Daga nan suka dora ta mashin suka kawo ta garin Mara dake cikin karamar hukumar Danmusa, suka kaita gidan Magaji na garin Mara ta lamba aka nemi yan uwanta aka gaya masu ta kubuta, daga nan aka mika ga Jami’an tsaro Sojoji suka dauko ta suka kawo ta Katsina ga sakataren Gwamnatin jihar Katsina Dr. Mustapha M. Inuwa, daga nan aka mika ta ga yan uwanta. Cikin su harda maigidanta Alh. Sale Hassan Musawa”.

Hadiza tana cikin yanayi na tashin hankali na irin hadarin data shiga cikin dajin nan tun daga lokacin da suka tafi da ita da lokacin da Allah ya kubuto da ita. “Hadiza ta bayyana cewa basuyi mata komi ba na cin zarafi, kawai dai suna tsare da ita suna gaya mata su kudi suke so, idan babu kudi zasu daure subar bata abinci harta mutu”. Barayin da suke tsare da ita suna tare da matan su da yayansu da Dabbobin su a cikin dajin”.

A yau din nan lahadi aka shirya kudi naira miliyan biyar (#5,000,000) don kai kudin fansa ga barayin a sako Hadiza bayan an kai masu miliyan daya da rabi (#1,500,000) suka amsa amma basu sako ta ba. Farkon da barayin suka tafi da Hadiza sun bukaci mijin Hadiza ya basu miliyan talatin kafin su sako mashi matar shi.

Rahoto. Surajo Yandaki
Mobile Social Media Crew
31/05/2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here